Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Zai Sayar Da Damar Shiga Amurka Na “Gold Card” Kan $5m


Attajirin wanda tsohon mai harkar cinikin gidaje ne yace za a tantance dukkanin mutanen da suka nemi sayen sabbin katunan kafin a sayar musu. 

A jiya Talata Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana shirinsa na sayar da sabbin katunan iznin zama a Amurka masu lakanin “katin zinare” akan kudi dala milyan 5 kowane-kuma manyan attajiran Rasha na iya samun cancantar saye.

Trump ya bayyana cewar cinikin sabbin katunan, wani nau’i ne na koren katin da aka saba amfani da shi mafi tsada, zai janyo mutanen da zasu samar da guraben aikin yi kuma za’a iya amfani da shi wajen cike gibin kasafin kudin Amurka.

“Zamu fara sayar da katin zinariya. Kai koren kati ne dakai, wannan katin zinariya ne. zamu sanyawa katin farashi na kimanin dala milyan 5,” kamar yadda ya shaidawa manema labarai a ofishin shugaban amurka.

Shugaban dan jam’iyyar republican, wanda ya baiwa batun korar bakin haure fifiko a wa’adin mulkinsa na 2, yace sabon katin zai zamo wata hanyar mutunta zama dan Amurka.

Za’a fara sayar da katunan nan da kimanin makonni 2, a cewar Trump.

Attajirin wanda tsohon mai harkar cinikin gidaje ne yace za a tantance dukkanin mutanen da suka nemi sayen sabbin katunan kafin a sayar musu.

Sai dai da aka tambaya ko attajiran kasar Rasha zasu iya neman sayen katin, Trump yace hakan abu ne me yiyuwa.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG