A ranar Litinin shugaba Donald Trump ya ce, yana gab da cimma kulla yarjejeniya da Ukraine da kuma Rasha domin kawo karshen yakin da ake yi a Ukraine, bayan yini guda da aka kwashe ana ganawa a fadar White House da shugaban Faransa Emmanuel Macron.
Trump ya bukaci Turai da ta dauki kaso mafi girma wajen samar da kudi, Paris kuma ta matsa kaimi wajen samun tabbaci daga Moscow.
Shugaban Amurka ya matsa kaimi kan burinsa na cimma yarjejeniyar kawo karshen yakin, wanda ya cika shekaru uku a ranar Litinin. Ya ce hakan zai hada da wata yarjejeniya da Ukraine game da muhimman albarkatun kasar ta, wata yarjejeniya da ya ce shugaban Ukraine na iya rattaba mata hannu nan da mako mai zuwa.
‘’Shugaba Trump ya kara da cewa, akwai rashin amintuwa daga dukkan sassan. "Shi yasa zuwa na a yanzu ya yi kyau. Amma ina ganin babbar cin riba naga Rasha na ta samar da yarjejeniya ta kuma cigaba da jagoranta a kyakkyawan tsari. Wannan shine abunda ya kamata ka yi kenan. To amma na yi Imani zai so kulla yarjejeniyar.’’
Macron ya lura da abunda kaje ya komo, inda ya ci gyaran Trump a ofishin Oval, a yayin da Trump ya ce Turai ta tallafawa Ukraine da bashi. Daganan kuma Macron ya yi gargadi game da yarda da Rasha.
Yace, a jira har a samu wani abu tukun, sannan a tantance, a duba a tabbatar, ya fada cikin halshen turanci. ‘’ Sannan mu tabbatar da cewa mun gina wadataccen tabbaci a dan kankanin lokaci. Kuma a nan ne muke shirye mu sa hannu. Game da Faransa kuwa, da dama daga takwarori na a Turai a shirye suke su sa hannu. To amma muna bukatar Amurka ta rufa mana baya, saboda hakan bangare ne na ingancin tabbaci kan tsaro.
Masu sharhi dai sun yi magana kan ainihin nasarorin da shugabannin biyu suka cimmawa a yayin ganawar ta su.
Dandalin Mu Tattauna