Manufar kwamitin da majalisar ta kafa ita ce ya gana da kungiyar kwadago da zummar shawo kan kungiyar ta dakatar da shiga yajin aiki yau Laraba.
Kodayake wa'adin da kungiyar NLC ta bayar bai cika ba amma sai kotun dake kula da dokokin ma'aikata ta ba kungiyar kwadagon umurnin ta dakatar da yajin aikin.
Wannan abun da kotun tayi Onarebul Ali Isa JC yace yayi daidai. Yace a akasarin gaskiya babu wanda zai goyi bayan a fantsama cikin yajin aiki domin zai sake dagula tattalin arzikin kasar. Yace rashin tuntubar masu ruwa da tsaki da gwamnati bata yi ba shi ya jawo cecekuce tsakaninta da kungiyar kwadago.
Ali Isa ya kira kungiyar kwadago da ta cigaba da tattaunawa domin a samu masalaha.
Amma Onarebul Muhammad Isa Jama'are yace batun karin kudin mai ba shi ne matsalar kasar ba, yana zargin akwai wata makarkashiya a kasa. Yace karamin ministan mai Dr Ibe Kachukwu baya taimakon shugaban kasa tsakaninsa da Allah.
Abubuwa sun yiwa shugaba Buhari yawa. Yace Kachukwu shi ne karamin ministan mai shi ne kuma babban daraktan kamfanin man fetur, shi ne kuma shugaban PPRA. Dokar da ta kafa kamfanin man fetur na kasa tace dole a raba mukaman. Dole Kachukwu ya saki mukami daya. A nemi wanda ya san harkokin kamfanin mai adalci a bashi shugabancin wurin.
Shi ma Onarebul Danlami Muhammad Kurfi yace talaka zai ci gajiyar karin kudin man din da aka yi amma fa sai an hada da hakuri.
Ga karin bayani.