Alhaji Ayuba Muhammad shugaban 'yan kasuwan arewacin Najeriya yace su 'yan kasuwa gaba daya ba sa goyon bayan yajin aikin da kungiyar kwadago take barazanar yi.
Yace su ba'a taba kiransu taro ba akan shirin wannan yajin aikin. Sun kira ilahirin duk 'yan kungiyarsu su cigaba da harkokinsu kada su damu da shiga yajin aiki. Alhaji Ayuba yace talakawa ba sa moran komi akan tallafin man fetur.
Ko a birnin Abuja ma kungiyar 'yan kasuwa ta Wuse ta bayyana adawarta da yajin aikin. Sakatarenta Alhaji Abubakar Abdullahi Dangara yace duk lokacin da aka yi yajin aiki kananan 'yan kasuwa ake jefawa cikin halin kakanikayi. Tun lokacin da ake batun cire tallafin mai talaka har yau yana cikin talauci. Masu karban kudin daga hannun gwamnati su ne suke jin dadi. Yace a cire tallafin domin sun yadda da shugaba Buhari.
Lokacin da aka cire tallafin Buhari yana shugaban PTF kowa ya gani a kasa. Yanzu da ya cire tallafin jama'a zasi gani a kasa.
Dangane da yadda mutane da kungiyoyi ke kushewa yajin aikin, Kwamred Ayuba Wabba shugaban kungiyar kwadagon Najeriya yace dama kodayaushe suka kira yajin aiki akan samu irin wadannan mutanen ko kungiyoyi. Sai dai yace kafin karin farashen mai buhun shinkafa nera dubu goma sha daya ne amma yanzu ya haura zuwa dubu goma sha uku. Yace dan kasuwan dake samun riba nikibaninki ba zai goyi bayan yajin aiki ba.
Ga karin bayani.