Masu zanga-zangar sun yi tururuwa a manyan hanyoyin Kaduna suna wakar yabawa Shugaba Buhari akan cire tallafin man fetur domin nunawa kungiyar kwadago cewa ba zasu amince da duk wani yajin aikin kin jini gwamnatin ba.
Alhaji Garkuwa Ibrahim Babur jagoran zugar wadanda suka aiwatar da zanga zangar yace sun fito ne domin 'yan kungiyar kwadago su fito su fada masu inda kudin kasar ke zuwa. Lokacin da aka kashe mutane a Maiduguri da wasu wurare me ya sa 'yan kungiyar kwadago basu fito sun yi zanga-zanga ba? Yace idan su 'yan halal ne su fito su yi yajin aiki kenan lokacin jifar Shaidan a Najeriya ya kusa.
Wasu dake cikin tawagar masu zanga-zangar sun ce 'yan kungiyar kwadago zasu sha jifa saboda matakin da gwamnatin Buhari ta dauka ya taimakawa talakawa ne. Dama can tallafin ba talaka yake taimakawa ba. Saboda haka sun gode da cireshi da aka yi. Sunce suna goyon bayan gwamnatin Buhari dari bisa dari. Kungiyar kwadago na bata lokaci ne kawai domin Buhari ba munafiki ba ne..
Wasu masu zanga zangar sunce idan kungiyar kwadago ta fito ashirye suke da duwatsunsu. Ko zasu mutu mutanen sun sha alwashin sai sun tunkari 'yan kungiyar kwadago koyaushe suka fito.
Alhaji Abdullahi Bayero mai taimakawa gwamnan jihar Kaduna Nasiru El-Rufai akan harkokin kungiyoyi da masu ruwa da tsaki shi yayi wa masu zanga-zangar jawabi a madadin gwamnan. Yace gwamnan ya so ya tarbesu da kansa domin yana alfahari da irin gudummawar da suka bayar da jajircewa akan matakin da gwamnatin Shugaba Buhari ta dauka to amma ayyuka ne suka yi masa yawa. Yace sakon da suka bada za'a mikashi ga shugaban kasa.
Ga karin bayani.