Kungiyoyin matasa da dama suka hadu domin bayyana bacin ransu akan matsalar karancin wutar lantarki da suke fama dashi a jihar tare da nuna yatsa kai tsaye ga kamfanin dake raba wutara wato Kadco dake Kaduna.
Matasan sun zargi kamfanin da ci da gumin talaka a jihar inda wasu anguwannin birnin Sokoto ke samun wutar sa'a daya kacal cikin kwanaki uku. Wasu yankunan ma basa samun wutar gaba daya.
Duk da rashin samun wutar hakan bai hana kamfanin cajin kudin wuta ba da tsadar gaske.
Kwamred Aminu Abdullahi shi ne ya jagoranci kungiyoyin wanda kuma ya zanta da manema labarai a madadin kungiyoyin. Yace sun samu labarin kamfanin na ba jihar Kebbi megawatts 47, jihar da bata kai yawan Sokoto ba. Wane dalili ya sa kamfanin ya yi hakan inda take ba Sokoto megawatts 16 maimakon ko ma 30 wanda zai iya taiakawa. Ko jihar Zamfara megawatts 21 ake bata.
Aminu yace cikin kwana uku da wuya mutum ya samu wutar awa daya a Sokoto. Dalili ke nan matasan jihar suka tashi su yaki lamarin.
Matasan sun ba kamfanin kwanaki biyar da ya shawo kan matsalar ko kuma ya gamu da fushinsu da zai haifar da matakin da ba zai yiwa kamfanin dadi ba.
A martanin da ya mayar babban jami'in kamfanin dake Sokoto Tijjani Mustapha yace matsalar karancin wutar lantarki matsala ce da ta shafi kasa baki daya.
Ga karin bayani.