Magoya bayan sun ce 'yan siyasa basu da tabbas a jamhuriyar Nijar domin koda an yi alkawari dasu sukan saba.
Shugaban KOPA, wato kawancen 'yan adawa, Malam Abdulmummuni yace abun da 'yan adawa suka yi na komawa majalisa da hukumar zabe haka halayen 'yan siyasar Nijar suke. Yawancin 'yan siyasar kasar basu da alkibla. Kowa na yin lissafin abun da zai samu ya gyarashi. Abun da zai tallafawa rayuwarsu suka sa gaba. Yace saboda haka ko an yi alkawari dasu sai su saba.
Shugaban KOPAn yace shi bai yi mamaki ba da matakin 'yan adawan maimakon haka ma ya jinjinawa jam'iyyar dake mulki bisa ga irin dagewar da 'ya'yanta suka yi. Yace sun yi shekaru ishirin suna dawa kafin su kama madafin iko. Amma a nasu bangaren sun ga wadanda suka barke suka bar jam'iyyar da ta basu mukami da can baya suka koma bangaren dake rike da mulki yau. Yace babu abun da basu gani ba.
A bangaren jam'iyyar PNDS Tarayya mai mulki Alhaji Gado yace tun farko wani mataki ne da 'yan adawan suka dauka wanda bashi yiwuwa. Amma su kam gaskiya suka tsaya kuma duk mai gaskiya yana tare da Allah. 'Yan adawa sun yi zargin cewa an yi sata a zabukan da suka gudana amma yau sun gani cewa gaskiya ta yi halinta.
Ga karin bayani.