Da kashi tasa’in da biyu da digo arba’in da tara ne hukumar zaben kasar Nijar CENI, ta bayana shugaba Issoufou Muhamadou, a matsayin wanda ya lashe zaben ashirin ga wata Maris, yayin da abokin fafatawarsa Hama Ahmadu, wanda ya bukaci magoya bayansa su kauracewa zaben ya sami kashi bakwai da digo hamsin da daya daga cikin dari.
Sai dai tuni ‘yan adawan suka nisantar da kansu daga sakamakon na ranar lahadin da ta gabata, hasalima sun ce a kaidance daga ranar daya ga watan Afrilu, mai zuwa Issoufou Muhamadou, ya gama wa’adin mulkin da ‘yan Nijar suka bash biyo bayan zaben da akayi a shekara 2011.
Tuni sabuwar alkiblar da bangarori siyasar ta Nijar suka dosa ta fara daukar hankalin kungiyoyin fararen hular kasar shugaban kungiyar Opele, Malam Lawali Abubakar, na ganin akwai bukatar gaggauta shirya taron sulhu..
Shi kuwa Abdu Alhaji Idi, wani dan rajin kare dimokradiya na ganin shugaban kasar ta Nijar Issoufou Muhamadou, ne keda nauyin hada kan jama’ar kasar domin magance kiki kakar dake neman maida hannun agogo baya.
Suma dai kungiyoyin kasa da kasa dake bin duddugin zabubbukan 2016, sun gargadi bangarorin siyasar ta Nijar,dasu bi hanyoyin sulhu domin dike barakar dake tsakaninsu.