Kungiyoyin sun bayyana cewa wani taron nazari da suka yi akan yadda alamuran mulki ke gudana a kasarsu ta Nijar sun gano alamomi masu karfi na kokarin da gwamnatin kasar keyi domin shimfida mulkin kama karya da talakawanta suka rungumi dimokradiya yau fiye da shekaru ishirin da biyar.
Saboda haka kungiyoyin sun kuduri yakar wannan sabon salon mulkin kasar da Shugaba Muhammad Issoufou yake shimfidawa.
Shugaban kungiyar Muliyan Sirajo Isa yana cikin masu jagorar yunkurin. Yace ba zargi suke yi ba abu ne na gaskiya, kuma tabbatacce a kasar. Misali, yace ba'a yi zabe ba. Wanda aka yi ba'a yishi kan tafarkin dimokradiya. An yi zaben ne bayan da aka yi watsi da kundun tsarin mulki da dokokin zaben kasar. An yi aiki da son kai tare da son rai saboda a biyawa mutum daya bukata, shugaban kasa na yanzu Muhammad Issoufou.
Amma shugaban kawancen kungiyoyin Rosel Abdu Mamman Lokoko mai goyon bayan gwamnatin Issoufou Muhammad na kallon korafin kungiyoyin rajin kare dimokradiya a matsayin mara tushe. Yace kashi sittin cikin dari sun zabi shugaban kasa na yanzu lamarin da ya bashi damar nada firayim minista kana shi kuma ya nada gwamnati.Yace duk wani dan kasa da ya tashi yace bai yadda da shirin ba to da doka yake fada. Idan su 'yan dimokradiya ne na kwarai ya kamata su duba abun da shugaban kasa keyi daidai wanda basu kuma kan ka'ida su kaiwa hukumomin dake kula da irinsu.
Kungiyoyin rajin kare mulkin dimokradiya din dai sun shirya yin zanga zanga ranar ishirin da hudu na wannan watan domin nuna rashin amincewa da salon tafiyar gwamnatin kasar..
Ga karin bayani.