A cikin jam'iyyar shugaban kasar Nijar na farko Diori Hamani wata dambarwa ce ta kunno kai saboda nada wasu 'yan jam'iyyar da gwamnatin kasar ta yanzu ta yi.
Jam'iyyar marigayi tsohon shugaban ta PPN RDA Giwa Giwa ta shiga rudani ne bayan wasu 'yan jam'iyyar suka yi zargin cewa wani bangaren jam'iyyar ne ke cin karensa ba babbaka a duk lokacin da aka zo raba mukamai a gwamnati.
Suna zargin cewa ko a yanzu haka lamarin yake tunda ba'a tuntubi 'yan jam'iyyar ba a lokacin da ta bada sunayen wasu a matsayin wakilanta a sabuwar gwamnatin shugaban kasar Muhammadou Issoufou.
Hajiya Aishatu Darmu ta Dogon Dutse tace abun da ya basu takaici shi ne yadda jam'iyya ta bada sunaye ba tare da kira taron jam'iyyar ba. Kamata ya yi shugaban kasa ya rushe wannan zabin domin a sake lale saboda akwai manyan 'yan jam'iyyar da suka sha wahala. Yakamata kowa ya sani kowa kuma ya ji domin su zabi wanda ya dace da suke so.Wadanda jam'iyyar ta tsayar ba'a sansu ba.
A cewar Alhaji Alkassim Sale dan kwamitin koli na jam'iyyar ta PPN RDA yace ba zata yiwu ba a ce duk matakin da jam'iyyar zata dauka sai ta je ta yi shawara a kasa da 'ya'yanta. Idan an yi hakan babu anfanin shgabanni ke nan.
Ga karin bayani.