Makon da ya gabata, Amadou ya sha kaye a zagaye na biyu na zaben shugaban kasa da shugaba Mahamadou Issoufou ya lashe, domin wa’adin mulki na biyu, da kashi casa’in da biyu cikin dari na kuri’in. Jam’iyun hamayya sun kauracewa zaben. Abinda yasa jam’iya mai mulki ta sami gagarumar nasara ke nan.
Wani kakakin jam’iyar hamayya yace, zargin kage ne da aka yi amfani da shi aka kama Amadou domin hana shi yin tasiri a zaben.
Kakakin jam’iyyarsa Ousseini Salatou yace, an kulle Hama Amadou aka hana shi yakin neman zabe. Ya yi fama da rashin lafiya a lokacin yakin neman zaben kafin a tafi da shi jinya a kasar Faransa kwana hudu gabanin zaben zagaye na biyu.
An kama kusoshin jam’iyun hamayya da dama tun daga watan Yuni shekara ta dubu biyu da goma sha hudu, bayanda ‘yan sanda suka kaddamar da bincike kan zargin safarar jarirai daga Najeariya da iyalan attajirai suke yi a Nijar. Matar Amadou na daga cikin wadanda aka kama, kafin daga baya aka sake ta.
Ranar Asabar za’a rantsar da shugaba Mohammadu Issofou domin wa’adin mulki na biyu na shekaru biyar.