Yanzu kasar ta Nijar tana da kotunan sauraren kararraki idan akwai rashin jittuwa tsakanin 'yan kasuwa ko kuma tsakaninsu da masu cinikayya dasu.
Kowacce matsala ta taso da ta shafi harakar kasuwanci da saye da sayarwa wadannan kotuna jama'a zasu mika kokensu.
Alhaji Sani Maikaset shugaban kungiyar 'yan kasuwar birnin Kwanni yace yakamata a ce kotun tana da reshe a koina a fadin kasar kuma a tabbata an bata kayan aiki.
Yace abu ne mai mahimmanci sosai a kafawa 'yan kasuwa kotu domin idan sun samu matsala da ta shafi kasuwanci sun san inda zasu nufa a warwareta. Duk wasu matsaloli da rikce-rikice kotun zasu nufa. Ya kira kotunan su ma su yi adalci tsakaninsu da Allah kuma a yi hukumci cikin lokaci kalilan. Yace a yi la'akari da cewa shi dan kasuwa da jari yake aiki, idan aka bata masa lokaci jarinsa zai samu rauni.
Su ma 'yan kasuwa sun nuna gamsuwarsu da kafa masu kotu na musamman. 'Yan kasuwan Kwanni birnin dake makwaftaka da Najeriya wanda kuma shi ne kan gaba a harkokin kasuwanci a Nijar sun nuna farin cikinsu da kafa kotun.
Ga karin bayani.