Kungiyar yaki da almundahana ta “Transparency International” shiyyar janhuriyar Nijar ta aika ma Shugaba Issouffou Muhammadou takardar bukatar ya gaggauta kawo karshen cin hanci da rashawa a jarabawar daukar ma’aikatan gwamnatin kasar.
Babban Sakataren INLC a kungiyar ta “Transparency International,” Malam Inwa Wada ya gaya ma wakilinmu a Niamey Souley Barma cewa bayan da Shugaba Issouffou Muhammadu ya samu wasikar tasu sai ya kira su ya basu tabbacin cewa zai gadar da kasa marar matsalar cin hanci da rashawa a karshen wa’adinsa.
Souley Barma ya kuma bayyana cewa Shugaban kasar ta Nijar ya umurci hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta binciki wannan zargin don daukar matakin da ya dace. Hasalima Barman ya ruwaito Mataimakin Shugaban Hukumar, Malam Salisu Uban Doman a cewa samun wasikar da Shugaba Issouffou Muhammadou ke da wuya.
Ga Souley Mummuni Barma da cikakken rahoton: