Daga cikin kujeru 171 na sabuwar majalisar dokokin kasar Nijar, 'yan majalisa 53 da yakamata su wakilci jama'a da sunan kawancen jam'iyyun adawa suke cigaba da kauracewa zaman majalisar wadda tuni ta fara gudanar da ayyuka masu mahimmanci.
Kauracewa zaman majalisar da 'yan adawan suke yi ya fara damun takwarorinsu na bangaren masu rinjaye irinsu Onarebul Seidu Amma na PNDS Tarayya. Yace an zabi 'yan majalisar ne saboda haka bayan zabe ba 'yan majalisar jam'iyyunsu ba ne amma 'yan majalisar talakawan da suka zabesu ne. Majalisa ta fara aiki fiye da makonni biyu ke nan amma sun cigaba da kasancewa suna zaune a gidajensu.
Seidu Amma yace 'yan majalisar 53 su sani akwai doka kuma tare dasu aka yi dokar. Yace idan mutum ya kaucewa zaman majalisa to akwai hukuncin da za'a yi masa har ya bar majalisar. Tunda ba'a sake dokar ba zasu yi anfani da ita akan wadannan 'yan majalisa 53 da har yanzu suna kauracewa zaman majalisar.
An bi hanyar laluma amma sun ki. Ana son su gane Nijar yau ta wahala saboda haka ya kamata su shiga zaman majalisa su yiwa kasar aiki.
Amma Onarebul Murtala Alhaji Mahmuda dan majalisar dokoki ne a karkashin jam'iyyar MNSD Nasara yace idan Allah ya yadda komi ya daidaita zasu shiga zaman majalisar su yi gwagwarmaya tare da takwarorinsu domin su samar ma kasar hakkinta. Akan ko ana iya hukumtar dasu bisa ga doka yace babu wata doka da ta tanadi hakan domin sun kauracewa zaman majalisar. Duk abun da za'a yi kan gaskiya zasu shiga majalisa su yi.
Ga karin bayani.