Gwajin makamin nukiliya da Koriya ta arewa ta yi yau Laraba, a kusa da sansanin jiragen karkashin ruwa na kasar da ke Sinpo, na nuna alamun sojojin kasar sun fara daukar matakan kariya daga barazanar harin ba-zata daga Amurka.
Dakarun Amurka da na Koriya ta kudu sun gano cewa an harba wannan makamin mai linzame guda daya da safiyar yau, a kusa da Sinpo dake kudancin lardin Hamgyong dake gabashin kasar.
Nazarin farko da aka yi ya nuna cewa makamin KN-15 mai matsakaicin zango ne aka harba. Sai dai kuma rundunar tsaron sararin samaniya ta arewa da ake kira NORAD ta ce gwajin makamin da aka yi daga Koriya ta arewa bai yi wata barazana ga nahiyar Amurka ta arewa ba.
Ita ma majalisar hafsoshin sojan Koriya ta kudu ta tabattarda cewa Koriya ta arewa ta harba makamin da aka ce yayi tafiya mai nisan kilomita 60.
Facebook Forum