Hotuna Kan Takaitattun Labaran Duniya Da Na Afirka a Yau
Hotuna Kan Takaitattun Labaran Duniya Da Na Afirka a Yau

1
‘Yan sanda sun kama mutane biyar da ake zargin na da hanu a wani hari da aka kai akan wasu daliban Najeriya hudu a New Delhi, harin da ya kai ga kwantar da su a asibiti. Ranar Alhamis 30 Maris 2017

2
Wata bas din coci ta murkushe mutane 12 har lahira a karamar hukumar Uvalde dake Jihar Texas. Ranar Alhamis 30 Maris 2017.

3
Firai Ministan Isra’ila Netanyahu na sa ran amince wa da gina sabbin gidaje a yamma da gabar Kogin Jordan nan da shekaru 20. Ranar Alhamis 30 Maris 2017.

4
Masu tsaron gabar tekun Italiya sun kai bakin haure 725 mafi yawancinsu ‘yan Afirka zuwa Sicily bayan da aka ceto su a tekun Meditareniya. Ranar Alhamis 30 Maris 2017.
Facebook Forum