Shugaban ya kara da cewa bayan tatsar bayanan ta bayyana sunansu saboda wata manufa ta siyasa, zargin da Rice ta fadi jiya Talata cewa "sam ba gaskiya ba ne."
A wata hira ta kafar labarai ta MSMBC, Rice ta ce babu kanshin gaskiya a zargin da Trump, ya yi a watan jiya cewa Obama, ya tatsi bayanan sirrinsa, zargin da 'yan majalisa da dama da kuma jami'an bangaren bayanan sirri su ka yi watsi da shi. To amma Trump, a wasu jerin sakonnin twitter, cikin kwanaki biyu da su ka gabata, ya yi ta nuni da wasu rahotannin da su ka nuna cewa Rice ta bayar da umurnin a tatsi bayanan sirri game da shi.
Rice ta ce a aikinta karkashin Fadar White House, ta kan yi nazarin bayanan sirri kulluyaumin. Ta kara da cewa, ba sabon abu ba ne ta bukaci masu tattara bayanan sirri su bayyana sunayen Amurkawan da aka ji su na zance da wasu mutanen kasashen waje a yayin tattara bayanan sirrin.
Ta ce daga bisani akan ba da irin wannan bayannan ga Sakataren Harkokin Wajen kasar da Sakataren Tsaro da kuma Shugaban Hukumar Bayanan Sirri na tsaron kasa a matsayin wani bangare na ayyukansu na kare Amurka.
Facebook Forum