Hukumomin garin Mocoa inda bala’in ya auku, sun fara mika gawarwakin wadanda hadarin ya rutsa da su ga iyalai da 'yan uwa domin a gaggauta yi masu sutura da kuma nufin kaucewa yaduwar cututtuka.
A daya bangaren kuma, masu ayyukan ceto na ci gaba da kokarin nemo mutane 200 da aka ce har yanzu ba a gansu ba.
Daga cikin mutane 273 da suka rasa rayukansu, 40 yara ne kanana.
Tuni dai shugaba Juan Manuel Santos, ya ayyana shirin farfado da yankin na Mocoa, inda ya yi alkawrin sake gina bututan ruwa da suka lalace dalilin zaizayar kasar.
A karshen makon da ya gabata ne, koguna da dama suka cika suka tumbatsa inda ta kai ga har sun haye tuddan gabarsu, lamarin da ya haifar da kwararar ruwa da laka da kuma baragizai, wadanda suka fada kan gidajen jama’a yayin da suke barci.