Kwamitin sulhun Majalissar Dinkin Duniya na wani zama na gaggawa yau Laraba don tattauna batun harin guba da aka kai a Siriyya wanda ya kashe mutane da yawa, a daidai lokacin da duniya ke Allah Wadai da wannan lamarin.
Wakilai, da jami’an diplomasiyya da kuma kwararru na dora laifin abinda ya faru a garin Khan Sheikhoun akan dakarun shugaba Bashar al-Assad da kawayensu na kasar Rasha. Hukumar lafiya ta duniya ta WHO, ta ce wadanda harin ya shafa na nuna alamun sun shaki gubar dake janyo illa ga jijiyar dan’adam.
Hadakar kungiyoyin bada agaji daga kasashen yammaci sun ce adadin wadanda suka rasa rayukansu ya kai dari, gubar ta kuma illata mutane fiye da dari uku da hamshin.
Rasha dai ta musanta taka rawa a wannan harin, ta na mai cewa jiragen yakin Siriyya ne suka kai hari akan wata ma’adana ko masana’anta mai ajiye makamai masu guba mallakin dakarun ‘yan tawaye.
Gwamnatin Siriyya ta nanata cewa bata taba yin amfani da makamai masu guba ba akan farar hula a duk shekaru 6 da aka kwashe ana yaki.
Facebook Forum