Wannan zabe shi zai nuna wanda kowa ne dan takara jam’iyyun za su fitar.
Bayan zaben na gobe Talata, ana sa ran fiye da juhohin Amurka 50 za su fitar dan takararsu, yayin da ‘yan takarar da ke baya-baya wajen kokarinsu na kamo abokanan hamayyarsu da ke gaba-gaba a jam’iyyun biyu wato Donald Trump da Hillary Clinton.
Wani lokaci kuma da za a kuma damar samun dumbin wakilai a zbukan share fagen zaben gama garin da za a yi shine na ranar bakwai ga watan Yuni, a lokacin da masu fashin baki su ke ganin ‘yan takara da ke baya-bayan sun Makara.
Yanzu haka Trumo na da wakilai 460, Ted Cruz na da 370, Marco Rubio na da 163 John Kasich kuwa na da 63.
A bangaren ‘yan Democrat kuwa, Clinton na da wakilai 1,231, yayin da abokin hamayyarta Bernie Sander ke da 576.
Clinton ya zuwa yanzu ta samu samu fiye da rabin adadin wakilan da a ke bukata wato 2,383.
A bangaren Republican kuwa ana bukatar dan takara ya samu wakilai 1,237.