Wannan muhawara wacce aka yi ta tsakanin ‘yan takara hudu da suka rage, ita ce ta karshe kafin wasu muhimman zabuka da za a yi a ranar Talata mai zuwa.
Kuma ba kamar sauran muhawarorin da suka yi a baya ba, wadanda suka ta’allaka akan sukar juna, ‘yan takarar sun yi wannan muhawar tare da nuna dattaku.
A lokacin da ya ke jawabinsa, Donald Trump, ya ce yana kan bakarsa kan kalaman da ya yi na cewa musulmi da dama ba sa kaunar Amurka, tare da shan alwashin cewa zai tura dakarun kasa dubu 30 domin yaki da mayakan IS a Gabas ta Tsakiya.
An kuma tambayi Turmp shin ko dukkanin Musulman duniya ne suka tsani Amurka? sai Trump ya ce “da yawa daga cikinsu sun tsani Amurka”. Ya kuma ce ba ya fargaba a ce yayi kuskure a kalamansansa.
Shi kuwa Marco Rubio cewa ya yi, hanya daya da za a iya yakar masu tsatsauran ra’ayi ita ce ta hanyar hada kai da Musulman da ba su da tsatsauran ra’ayi.
Sanata Ted Cruz ana shi jawabin, ya soki maslahar da Trump ya gabatar kan batun masu tsatsauran ra’ayi da sha’anin cinikayya, inda ya ce ba su da alkbila.