Babbar kotun tarayya dake Kano ta bada belin shugaban masu rinjaye na Majalisar Wakilan Najeriya, Alhassan Ado Doguwa, wanda ke fuskantar tuhumar kisan kai da rike makami ko mallakar makami babu izinin hukuma.
Tawagar dan takarar jam’iyyar PDP a babban zaben 2023 Atiku Abubakar, ta gudanar da zanga-zangar lumana zuwa hukumar zabe don nuna rashin amincewa da sakamakon zaben.
Rundunar 'yan sanda a jihar Kano ta ce ta bankado wani yunkuri da wasu batagarin ‘yan siyasa ke yi na shiga da makamai cikin jihar, domin amfani da su a yayin zaben gwamna da na ‘yan majalisar dokokin jihohi da za’a yi ranar Asabar mai zuwa
Kungiyar kiristocin Najeriya (CAN) reshen matasa a arewacin kasar ta bukaci duk mabiya su kwantar da hankalin su biyo bayan ayyana Bola Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa a Najeriya.
Kotun daukaka kara ta bai wa dan takarar jam'iyyar PDP Atiku Abubakar da na jam'iyyar Labour Peter Obi hurumin hukumar zabe ta ba su dama su binciki kayan da a ka yi amfani da su wajen gudanar da babban zaben 2023.
Bayan ayyana ‘dan takaran jamiyar APC Bola Ahmed Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa da aka gudar a ranar asabar 25 ga watan Fabrairu, an fara wasu shagulgulan murna.
Rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano ta ce da ta kammala bincike za ta gurfanar da shugaban masu rinjaye na majalisar wakilan Najeriya Alhassan Ado Doguwa a gaban kotu.
Wasu 'yan adawa sun fice daga dakin gabatarwa da sanar da sakamakon zaben shugaban Njaeriya, don rashin gamsuwa ga yadda a ke gabatar da sakamakon.
Turawan zabe a Najeriya na ci gaba da bayyana sakamakon zabe a matakin kasa da jihohi da kuma mazabun ‘yan majalisar dokokin Kasar.
Yayin da ‘yan Najeriya suka zaku don jin sakamakon zabubukan da suka yi, wani abu da ke daukar hankali shine yadda ake samun soke sakamakon wasu runfuna abin da ke sa ba a iya ayyana dan takarar da ke da galaba amazabun.
Wakilan jam'iyyun hamaiya sun yi watsi da yadda a ke gabatar da sakamakon zaben shugaban Najeriya a wuni na biyu da fara gabatar da sakamakon.
Hukumar zaben Najeriya ta karbi sakamakon zaben shugaban kasa daga jihar Ekiti, wacce da ma ta kan zama ta farko a wajen tura sakamako.
Domin Kari