Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yan Adawa Sun Fice Daga Dakin Tattarawa Da Sanar Da Sakamakon Zabe


Zauren Gabatar Da Sakamakon Zabe
Zauren Gabatar Da Sakamakon Zabe

Wasu 'yan adawa sun fice daga dakin gabatarwa da sanar da sakamakon zaben shugaban Njaeriya, don rashin gamsuwa ga yadda a ke gabatar da sakamakon.

Wakilin PDP Dino Melaye, da na LP Umar Ibarhim, da masu mara mu su baya sun tashi daga kujerun su, su ka fice su na cewa ba ma za su sake sauraron sakamakon ba don ba adalci a ciki, musamman sun ce an ki nuna sakamakon allo da na'urar hana magudi ta BVAS ta dauka.

Duk da haka wakilin jam'iyyar hamaiya ta NRM Zaphaniah A Jisalo, da ke marawa APC baya ya tsaya tare da wasu 'yan hamaiya da ba sa ganin wani kuskure da a ka aikata.

Jisalo, ya ce ya ga dan takarar sa na jam'iyyar NRM ba zai kai labari ba, don haka ya ga gara ya marawa dan APC baya.

Da alamu manyan 'yan adawar sun yi bankwana da dakin sakamakon watakila sai dai a gamu a kotu.

Domin Karin bayani ga rahotan Nasiru Adamu El-Hikaya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00

XS
SM
MD
LG