Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Buhari Ya Yi Jawabinsa Na Karshe A Zauren Majalisar Dinkin Duniya


Shugaba Buhari a lokacin da yake gabatar da jawabinsa a zauren Majalisar Dinkin Duniya (AP)
Shugaba Buhari a lokacin da yake gabatar da jawabinsa a zauren Majalisar Dinkin Duniya (AP)

“Yanzu haka muna shirin gudanar da zabe a watan Fabrairu mai zuwa, taron Majalisar Dinkin Duniya da za a yi (badi) a karo na 78, bakuwar fuska za ku gani a nan yana magana da yawun Najeriya.” In ji Buhari.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi ban-kwana da zauren Majalisar Dinkin Duniya yayi da yake gabatar da jawabinsa.

Wannan shi ne karo na karshe da shugaban na Najeriya zai halarci babban taron majalisar wanda ake yi a karo na 77 a birnin New York da ke Amurka.

A watan Mayun badi, Buhari zai kammala wa’adin mulkinsa na biyu yayin da Najeriya wacce ita ce kasa mafi yawan al’uma a nahiyar Afikra take shirin gudanar da babban zabe a watan Fabrairu.

“Yanzu haka muna shirin gudanar da zabe a watan Fabrairu mai zuwa, taron Majalisar Dinkin Duniya da za a yi (badi) a karo na 78, bakuwar fuska za ku gani a nan yana magana da yawun Najeriya.” Buhari ya fada a ranar Laraba a lokacin da yake gabatar da jawabin nasa.

A cewar Buhari, “mu muna mutunta tsarin wa’adin mulki da doka ta tanada, muna kuma bin wannan tsari sau da kafa. Mun ga irin mummunan tasirin da aukuwa idan shugabanni suka yi yunkurin sauya kundin tsarin mulki.”

Gabanin wadannan kalamai, shugaban na Najeriya har ila yau, ya tabo batutuwan tattalin arziki, cutar COVID-19, sauyin yanayi da kuma irin rawar da Najeriya take takawa wajen tabbatar da wanzuwar zaman lafiya a kasashen nahiyar Afirka.

XS
SM
MD
LG