A kasar Guinea, majinyata da dama suna rungumar hanyar kiwon lafiya na gargajiya domin kula da lafiyar su, kazalika, akwai masu irin wannan sana’ar da dama a babban birnin kasar na Conakry.
Zainab Ujudud Shariff kwararriya kan magungunan gargajiya a Najeriya kuma tsohuwar daraktar Sashin Bunkasa Maganin Gargajiya a Ma’aikatar Lafiya ta Najeriya, ta yi mana karin bayani a game da alfanun magungunan.
Maganin gargajiya ya kunshi abubuwa da dama na gargajiya da na zamani wanda ya samo tushe daga al’adun gargajiya da ake amfani da su tun iyaye da kakanni wajen kariya, ganowa da kuma magance jerin cututtuka na bayyane da kuma cututtukan tabin hankali, a cewar kungiyar hukumar ta Duniya WHO.
Wadannan bala’o’I suna faruwa ne lokaci guda sannan suna kai wa ga yiwa mutane rauni, haifar da barazanar lafiyar al’umma sannan su haifar da mumunar barna da asara dake haifar da matsala wajen samar da kulawa ga wadanda suke da bukata.
Abdulshahid Sarki, Kwararren likita a asibitin kasa dake Abuja, ya yi mana bayani a game da matakan da suka kamata mutane su dauka don tunkarar al’amari na daukin gaggawa.
Ra’ayoyin wasu mutane daga Najeriya game da irin matakan gaggawa da suke dauka na taimakon kan su idan bukata ta taso.
Bala’o’I na iya faruwa kwatsam, a ko yaushe ba tare da wani shiri ba. Mummunar guguwa, ambaliyar ruwa da girgizar kasa na daga cikin bala’o’in da suke aukuwa da suke jefa al’umma cikin tashin hankali.
Bisa binciken cibiyar kiwon lafiya ta Amurka, samun isashen bacci yana inganta yadda kwakwalwa take aiki, yanayin farin ciki da kuma lafiyar ka. Rashin sammun wadatacen bacci yana kara barazanar kamuwa da cututtuka da matsalolin lafiya da dama kamar cututtukan zuciya.
Wasu mutane mazauna birnin Jos sun bada ra’ayoyinsu game da matsalar miyagun kwayoyi, a inda suke da kuma irin taimakon da yakamata a baiwa masu ta’ammali da kwayoyi.
Wasu mutane mazaunan Jamhuriyar Nijar, sun bada ra’yoyinsu.
Da Dr Sabo Ahmad, Farfesa a Kwalejin Ilimin Kimiyyar Lafiya Jami’ar Jos ya yi karin bayani a game da girman matsalar shakar gurbatacciyar iska da kuma hanyoyin kariya.
Sakamakon yakin da aka kwashe sama da shekaru 30 ana yi, ‘yan Somaliya na da raunuka da dama, na bayyane da wadanda ba a iya gani. Binciken da Majalisar Dinkin Duniya da ma'aikatar lafiya ta Somalia da jami'ar kasar suka gudanar ya nuna cewa matsalar tabin hankali a tsakanin matasa ta fi yawa.
Domin Kari