Wadannan bala’o’I suna faruwa ne lokaci guda sannan suna kai wa ga yiwa mutane rauni, haifar da barazanar lafiyar al’umma sannan su haifar da mumunar barna da asara dake haifar da matsala wajen samar da kulawa ga wadanda suke da bukata.
Abdulshahid Sarki, Kwararren likita a asibitin kasa dake Abuja, ya yi mana bayani a game da matakan da suka kamata mutane su dauka don tunkarar al’amari na daukin gaggawa.
Ra’ayoyin wasu mutane daga Najeriya game da irin matakan gaggawa da suke dauka na taimakon kan su idan bukata ta taso.
Bala’o’I na iya faruwa kwatsam, a ko yaushe ba tare da wani shiri ba. Mummunar guguwa, ambaliyar ruwa da girgizar kasa na daga cikin bala’o’in da suke aukuwa da suke jefa al’umma cikin tashin hankali.
Bisa binciken cibiyar kiwon lafiya ta Amurka, samun isashen bacci yana inganta yadda kwakwalwa take aiki, yanayin farin ciki da kuma lafiyar ka. Rashin sammun wadatacen bacci yana kara barazanar kamuwa da cututtuka da matsalolin lafiya da dama kamar cututtukan zuciya.
Wasu mutane mazauna birnin Jos sun bada ra’ayoyinsu game da matsalar miyagun kwayoyi, a inda suke da kuma irin taimakon da yakamata a baiwa masu ta’ammali da kwayoyi.
Wasu mutane mazaunan Jamhuriyar Nijar, sun bada ra’yoyinsu.
Da Dr Sabo Ahmad, Farfesa a Kwalejin Ilimin Kimiyyar Lafiya Jami’ar Jos ya yi karin bayani a game da girman matsalar shakar gurbatacciyar iska da kuma hanyoyin kariya.
Sakamakon yakin da aka kwashe sama da shekaru 30 ana yi, ‘yan Somaliya na da raunuka da dama, na bayyane da wadanda ba a iya gani. Binciken da Majalisar Dinkin Duniya da ma'aikatar lafiya ta Somalia da jami'ar kasar suka gudanar ya nuna cewa matsalar tabin hankali a tsakanin matasa ta fi yawa.
Bisa kididdigar da hukumar lafiya ta duniya WHO ta fitar, kusan dukkan mutane a duniya suna shakar iskar da ta zarce ka'idojin ingancin iska na hukumar lafiya ta duniya – wato isa da take a gurbace. Wannan gurbacewar yanayi na da illa ga lafiyar dan adam.
Mai daukan hoton y ace tun lokacin da ya gano muhimmancin daukar hoto kuma da ma yana aiki a matsayin marubuci ta bangaren tallace-tallace, sai ya ji komai ya yi daidai. Yana da baiwa biyu da yawancin mutane ba su da su. To me yasa ba zai hada wadannan basirun ba wajen ba da labarai a nahiyar?
Dr Fatima Zara Umate, Likita A Asibitin Kwararru Dake Maiduguri a Najeriya ta yi karin haske a game da lalurar, da kuma hanyoyin magance ta.
Domin Kari