Binciken Da Aka Yi a Kan Lafiyar Kwakwalwa a Somaliya Ya Nuna Kashi 77% Na Al'ummar Kasar Na Da Matsalar Kwakwalwa
Sakamakon yakin da aka kwashe sama da shekaru 30 ana yi, ‘yan Somaliya na da raunuka da dama, na bayyane da wadanda ba a iya gani. Binciken da Majalisar Dinkin Duniya da ma'aikatar lafiya ta Somalia da jami'ar kasar suka gudanar ya nuna cewa matsalar tabin hankali a tsakanin matasa ta fi yawa.