Shirin ya mafia hankalo kan kafewar jinin al’ada na mata wato menopause da kuma daukewar sha’awa da kwayoyin haihuwa a maza wato Andropause.
Shirin lafiyarmu na wannan makon, ya mai da hankali akan cututtukan Kansar da suka fi addabar mata a fadin duniya.
Hukumar Lafiya Ta Duniya ta sahalewa sabon maganin rigakafin zazzabin cizon sauro. Ana fatan za a gaggauta fitar da sabon maganin a kasashen Afirka a cikin watanni masu zuwa.
Dr. Hajara Asheikh Jarma, kwararriyar jami’ar lafiya a asibitin koyarwa na jami’ar Maiduguri, ta yi wa wakilyar mu Hussaina Muhammed karin bayani a game da masu fama da lalurar zabiya.
Usman Audu, wani mai lalurar zabiya a birnin Maiduguri na Najeriya, ya yiwa Muryar Amurka karin bayani a game da kalubalen da suke fuskanta.
Kwararru sun ce a sa’ilin da shekarun mutane su ke ja, ya yiwu su fuskanci matsalolin lafiyar da suka zama ruwan dare tsakanin dattawa kamar yanar ido, rashin ji, cutar sukari, ciwon baya da na wuya.
Wani dattijo mazaunin Abuja mai suna Tanko Yakasai, wanda ya tasam ma shekaru 100 a duniya. Ya yi mana bayani game da yadda yake kula da lafiyar shi.
Kwararu sun ce asa’ilin da shekarun mutane suke ja, ya yiwu su fuskanci matsalolin lafiyar da suka zama ruwan dare tsakanin dattawa kamar yanar ido, rashin ji, cutar sukari, ciwon baya da na wuya.
A al’ummar kasashen Afirka, tsofaffi suna da daraja da mahimmanci wajen raya al’adun gargajiya kana suna kasancewa tamkar madubin duba ga matasa. Ko da yake, tsufa na zuwa da irin nasa kalubaloli daban-daban da suka hada da matsalolin lafiya da kuma wadatattacen kulawar lafiya.
Majalisar dokokin Ghana ta kada kuri’ar da za ta bada dama a hukunta duk wanda ya zargi tsofaffi da maita. Idan a ka yi nasarar tabbatar da sabuwar dokar, za ta bada dama a rufe sansanonin sama da mutane 500 da ake zargi da maita.
A kasar Guinea, majinyata da dama suna rungumar hanyar kiwon lafiya na gargajiya domin kula da lafiyar su, kazalika, akwai masu irin wannan sana’ar da dama a babban birnin kasar na Conakry.
Zainab Ujudud Shariff kwararriya kan magungunan gargajiya a Najeriya kuma tsohuwar daraktar Sashin Bunkasa Maganin Gargajiya a Ma’aikatar Lafiya ta Najeriya, ta yi mana karin bayani a game da alfanun magungunan.
Domin Kari