“Wannan ya zamanto wani abu ne da jami’yyun biyu suka maida hankali akai cikin tsawon lokaci,” in ji Alex Contant, mazaunin birnin Washington da ya kware a fannin tsare-tsare a Jam’iyyar Republican wanda kuma ya taba zama sakataren yada labaran jam’iyyarsa a kwamitin kasa a 2008.
Jam’iyyar Democrat ta fi maida hankali wajen nuna goyon baya ga tsirarun al’umomi, a cewarsa, ko da yake, kamar yadda jaridar Politico ta ruwaito a watan Yuli, sai da aka yi ca akan kusoshin jam’iyyar a shekarun da suka gabata kafin su fara amincewa da ‘yan takara bakaken fata a yankunan da bakaken fatar ba su da rinjaye.
Alex Conant, Mai yi wa Republican tsare-tsare: ‘Duk wanda yake so ya yi takara (siyasa) ya yi takararsa’ (Skype/VOA)
Mai yiwuwa jam’iyyar Republican “sai ta yi tukin tsaye a nan gaba,” a cewar Contant.
“Kasarmu na da girma da al’umomi iri-iri. Idan har za ka lashe zabe, zai yi kyau ka fito daga cikin al’umomi daban-daban ko kuma ka wakilci al’umomi da za su kada kuri’a. ………hakan kuma na nufin sai ka nemi karin ‘yan takara daga al’umar bakaken fata.”
Amma ta yaya masu burin shiga siyasa wadanda ba fararen fata ba – musamman sabbin zuwa Amurka, za su iya samun tikitin takara?
A cewar Naquette Ricks, wacce na daya daga cikin ‘yan farko-farkon zuwa Amurka daga Afirka, da ke takara - a matakin karamar hukuma zuwa Majalisar Dattawa, samun horo, na da matukar muhimmanci.
Ricks tana takarar neman kujerar Majalisar Wakilai a Colorado. Kungiyoyi da dama sun taimaka mata wajen sa ta a hanya, ciki har da kungiyar New American Leaders, wacce ba ruwanta da jam’iyya, da kuma Emerge, wacce ke kimtsa mata don su tsaya takara a matsayin ‘yan Democrats.
“Sun koya mana yadda za mu tara kudade, yadda za mu gabatar da kanmu, da yadda za mu rubuta jawabinmu. In ji Ricks tana mai cewa, “dukkan wadannan batutuwa suna da muhimmanci, saboda idan ka fita yin takara mutane za su san cewa ba wasa kake yi ba kuma mutane na sauraro.”
Naquetta Ricks, ‘yar asalin kasar a Liberia da ke neman takara a Colorado, ta ce horon da ta samu ya sa ta kware wajen iya tara kudaden kamfe. (Skype/VOA)
Ricks tana ‘yar matashiya, ita da iyayenta suka tsere daga kasarsu da sojoji suka yi juyin mulki.
A matsayinta na ‘yar kasuwa da ke renon ‘ya’yanta ita kadai kuma bakuwa, Ricks tana so a fito da matsalolin da ke addabar Gundumarsu, wacce ta hada da yankin Aurora da ke wajen birnin Denver.
“Yankin ne mai al’umomi daban-daban,” a cewarta. “Mutum daya da cikin kowane mutum biyar zai ce maka daga wata kasa yake, ko daga China ko Burma kake ko kudancin Amurka ko Afirka, duk mun fito ne daga wurare daban-daban.”
A cewar Davisha Johnson, masu aikin yakin neman zabe ma na bukatar a dora su a hanya.
Shekara hudu da suka gabata, ta bude wani shagon sayar da kayan kwalliya a kusa da Atlanta da ke jihar Georgia.
Wurin a karamar hukumar da ake kira Gwinnett yake, yankin da ya ga karin al’umar bakaken fata da bakin haure – ciki har da na Afirka ke karuwa tun daga shekarun 1990.
“Na lura cewa, ina bukatar na kirkiri hanyar da za a horar, a ilimantar da masu sha’awar ‘yan takarar,” in ji ta.
Domin sanin mamakar yadda ake tafiyar da harkar yakin neman zabe, Johson ta shiga “wuraren da ake samun horo kan siyasa. ……….. hakan ya ba ni damar samun kwarewa sosai.”
Johnson ta taimakawa wasu ‘yan takara samun nasarar lashe zabe, kama daga kwamitin karamar hukuma zuwa babbar kotun Georgia da majalisar dokokin jiha a jihohin Georgia da Tennessee.
‘Abin Mai Yiwuwa Ne’
‘Yan takarar da suka kasance sabbin zuwa a Amurka, su kan fuskanci kalubale na daban wajen gudanar da yakin neman zabe.
“Dole sai mutum ya iya tara kudi,” a cewar Conant, mai tsare-tsare a jam’iyyar Republican. “Ina kuma ganin ba lallai ba ne bakin da suka zo da farko, ba su da hanyoyin samun masu ba su tallafin kudi idan ka kwatanta da wanda ya riga ya kafu.”
“Sannan, ba lallai ba ne a ce an san su, domin ba su jima a Amurka ba,” hakan zai sa ba za kasance suna da hanyoyi kamar na abokanan gogayyarsu.
“Sai dai, muna ganin karin bakin da suka zo da farko suna neman takara kuma suna samun nasara,” a cewar Conant. “…… saboda haka, lallai abu ne mai yiwuwa, duk da cewa ba abu ne mai sauki ba.”
‘Yan takarar da ke da alaka da nahiyar Afirka, za su iya amfani da jama’ar nahiyarsu da ke zaune a nan, a cewar Johnson.
“Daya daga cikin hanyoyin da ‘yan Afirka suka yi zarra ita ce, suna da tarin jama’a, a cewarta. “Abu na farko baya ga batun kudi shi ne, dole ka samu masu goyon bayanka. Mutane a can gida na cewa, ina da dan uwa a Maryland. Ina da dan uwa a Texas.’ Kana da mutane da za su rika yi maka waya, da wadanda za su rika aika maka sa sakonnin tes. Kana kuma da mutanen da za su fita maka ranar zabe.”
Sai dai har yanzu akwai kalubale.
Annobar coronavirus ta sa an dakile yakin neman zabe ga kowanne dan takara, wanda zai fi shafar musamman sabbin masu takara da ke son su gabatar da kansu ga masu kada kuri’a.
Sannan a sassan kasar, ‘yan takarar da ba fararen fata ba, na fuskantar wariyar launin fata a kaikaice, da yadda ake kallon ‘kwarewarsu,’ da wahalar tara kudin kamfe da kuma shakku da kusoshin jam’iyyu ke nunawa a kansu,” kamar yadda jaridar Politico ta wallafa a watan Yuli.
Sai dai wannan zabe ya bijiro da batun rashin daidaito a tsakanin jinsuna, abin da Kojo Asamoa Caesar ya ce ya taimakawa yakin neman zabensa wajen ka da dan majalisar Oklohoma mai ci Kevin Hern wanda dan Republican ne.
‘Mutane Sun Goya Mana baya’
Zanga zangar da ta watsu sanadiyyar mutuwar George Floyd, wani bakar fata da ya samu mummunan raunin da ya kai mutuwarsa a lokacin da ya ‘yan sanda kama shi a birnin Minneapolis da ke jihar Minnesota a watan Mayu, “ta yi karo da kaimin yakin neman zabenmu,…. wanda mafi aksari mata fararen fata suka mara mana baya. Hakan ya taimaka wajen ba mu nasara.
Asamoa-caesar, malami ne da aka haifa a Amurka iyayensa daga Ghana suka zo, ya kasance bakar fata na farko dan Democrat ba’amurke dan asalin Ghana da da aka zaba a gundumarsa, wacce ta hada da Tulsa, birnin da ke kokarin duba tarihinsa kan kisan gillar da aka yi wa Amurkawa bakaken fata ‘yan asalin Afirka a shekarar 1921.
Yinka Faleti daga Legas Najeriya da ya tsaya takarar a jihar Missouri ya sha gwaggwarmaya kafin ya kai ga wannan matsayin.
Ya dawo Amurka ne yana dan shekara bakwai, bayan shekaru da dama sai ya samu mukami a Makarantar Sojin Amurka a West Point, makaranta mafi daukaka ta sojoji.
Ya yi aiki na shekara shida a matsayin sojan da ke kula da kayan yaki da ya hada da zuwa aikin soja sau biyu a yankin Gabas ta Tsakiya.
Amma bayan ya bar soja, ya fita da digiri na Lauya kuma yana aikin zaman kansa a matsayin mai daukaka kara a matakin jiha, wani abu na daban ne ya saka shi neman ya ba da gudumawa.
A shekarar 2014 wani harbi da aka yi wa matashi Micheal Brown da wani jami’in dan sanda ya yi a Ferguson, Missouri shi ya tunzura Faleti ya fara nazarin yadda zai ba da gudunmowa.
Yana so ya taimaka wajen kawo daidaito da yake gani a cikin al’umma.
Ko ma da mene ne, duk abin da ya faru a ranar zabe, samun ilimin yin takarar, zai iya zama makami wajen yin kamfe a nan gaba.
A cewar Conant, “duk wanda yake sha’awar yin takara, to ya fito ya yi takara. Hanya daya da za ka iya kwarewa a matsayinka na dan takara shi ne ka yi takarar.”
Wadanda suka taimnka wane rubuta wannan labari a Sashen Afirka na VOA: Ayen Bior, James Butty, Peter Clottey, Esther Githui Ewart, Carol Guensburg, Sahra Eidle Nur da Venuste Nshimiyimana. Mahmud Lalo ya Fassara.
Facebook Forum