An bude wani sabon babi a takaddamar sakamakon zaben Shugaban Kasa a Najeriya, bayan da jam'iyyar PDP ta shigar da kara a kotun daukaka kara don kalubalantar ayyana Shugaba Buhari na jam'iyyar APC da aka yi a matsayin wanda ya ci zaben.
Jayayya kan makomar zaben gwamnan jahar Bauci sai abin da ya yi gaba, duk kuwa da shirin bayyana sakamakon zaben a yau dinnan, bayan da hukumar zabe ta INEC ta sauya shawara ta wajen tsame jahar Bauci daga jerin jahohin da ta ayyana zabukansu marasa kammala.
Jami’iyyar PDP a jahar Nasarawa ta ce za ta je kotu saboda rashin gaskiya da ta ce anyi mata a zaben gwamna da aka gudanar makon jiya.
Sabbin ‘yan Majalisar Dattawa da za su sha rantsuwar fara aiki cikin ‘yan Majalisa 109 a Majalisa ta 9 tun 1999, na cewa kasancewar su sabbi hakan ba za ta sa su koma tamkar ‘yan kallo a Majalisar ba.
Bayan da hukumar zaben Najeriya ta fitar da sanarwar ranar da za a gudanar da zabukan da ba a kammala ba, jam'iyyar APC mai mulki da kuma babbar jam'iyyar adawa ta PDP, kowacce ta nuna kwarin gwiwar cewa ita za ta samu nasara.
Wasu mata magoya bayan dan takarar gwamana na jam'iyyar PDP a jihar Bauchi, Bala Muhammad Duguri (Kauran Bauchi), sun yi wata zanga zangar lumana a kan titin zuwa hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta reshen jihar.
Biyo bayan nasarar lashe zaben da gwamnan jihar Taraba, Akitek Darius Dickson Isiyaku na PDP ya yi, yanzu haka wata sabuwa ta kunno kai inda dan takarar APC a jihar ya ce ba zata sabu ba.
Domin Kari