Yayin da hukumar zaben Najeriya ke harmar bayyana sakamanon zaben gwamnan jahar Bauchi a yau dinnan Talata bayan tsame jahar daga jerin jahohin da ta ayyana zabukansu marasa kammala, jam’iyyar APC mai mulki ta ce ba zai sabu ba.
Wasu jigajigan Jam’iyyar APC a Abuja sun ce ba za su amince da sauya matsayi da hukumar za6e ta yi na amincewa da ingancin sakamakon zaben Karamar Hukumar Tafawa Balewa ta Jahar ba domin, a cewarsu, akwai wasu tambayoyi da dama da ya kamata Kwamitin Bincike da INEC ta kafa a karkashin jami'inta, Festus Okoye, ya amsa kafin a dau wannan mataki wanda, a cewarta, mayar da hannun agogo baya ne, kuma Hukumar INEC ba ta da hurumin yin amai ta lashe irin haka.
Wata mamban Kwamitin Yakin Neman Zabe na Kasa na Jam’iyyar APC din, Hajiya Rabi Sulu Gambari ta ce ba a yi wa APC adalci ba domin ai sakamakon za6en an ce an yayyaga shi, idan haka ne wane ne hukumar zabe za ta yi amfani da shi wajen fadin sakamako?
Irin nasarar da APC ta samu a zaben shugaban kasa da na 'yan majalisun tarayya shi ne ya sa APC ke ganin Jam’iyyar adawa da Hukumar za6e sun shirya magudi ne a karamar Hukumar Tafawa Balewa, wani abu da mai magana da yawun Jam’iyyar PDP Umar Sani (De Cat) ya karyata, inda ya ce PDP ce ke da rinjaye a kuri'un da aka riga aka wallafa, saboda haka abu ne mai wuya su yarda da wani zargin cewa za su yi wani magudi tunda su ke da rinjaye.
Amma a tsokacinsa kan wannan al'amarin, kwararre a fannin Kundin Tsarin Mulki Barista Mainasara Umar, ya ce akwai tanade tanade da kundin tsarin mulki ya yi cewa a yi bincike kafin a cimma matsaya, amma Kwamitin da Hukumar Za6e ta nada ya ce ai Karamar Hukuma daya ce da ba za ta sauya komi a sakamakon za6en Gwamna ba, shi ya sa aka fasa maimaita za6e a wurin, kuma hukumar za6e ta na da wannan hurumin.
Fadar Shugaban Kasa dai ta ce Hukumar za6e ce ke da hurumin yin komi a harkar za6e a kasar, saboda haka ba za ta sa baki a al'amarin ba.
Ga Madina Dauda da cikakken rahoton:
Facebook Forum