Wasu da ba'a san ko su wanene ba sun Harbe dan takarar Sanata a tutar jam'iyar ADP, Hon. Temitope Olatoye (Sugar) a Jihar Oyo.
Matsalar na'urarar tantance masu kada kuri'a da kuma saye ko saida kuri'a na daga cikin batutuwan da masu sa ido na cikin gida suka koka akai dangane da zaben gwamnoni da akai jiya a Najeriya.
Wasu 'yan kunar bakin wake da ake zargin 'yan kungiyar Boko Haram ne yi kokarin kai hari a wani Cocin Katolika dake burnin Shawu, dake jihar Adamawa.
A jihar Sakkwato an sami fitowar jama'a sosai a runfunan zabe, sabanin jahohin Zamfara da Kebbi.
Mata da masu fama da lalurar nakasa na daga cikin dubban mutanen da sukayi tururuwa zuwa rumfunan zabe domin kada kuri'ar su a zaben Gwamna da 'yan Majalisar Dokokin Jihar Neja a Najeriya.
A jihar Katsina kayan aiki da ma’aikatan zabe tare da wakilan jam’iyyu wato “Agent” da kuma jami’an tsaro duk sun isa tashoshin zabe da wuri.
rahotannin dake fitowa daga birnin Legas na nuna cewa mutane da dama basu fito ba domin zabe, duk da yake an gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali da lumana a birnin.
An samu karancin fitowar masu zabe a wasu sassan jihohin Adamawa da Taraba, a zaben gwamnoni da na 'yan majalisar dokokin jihohi da ake yi yau Asabar, a Najeriya.
Manyan ‘yan takara na jam’iyyu APC da PDP da sauran jam’iyyu fiye da 50 na fafatawa a neman kujerar gwamnan Kano, sai dai 'yan sanda sun kama wata mota makare da takardu da ake zargin kuri'un zabe ne.
Rahotanni daga jihohin Bauchi da Gombe na cewar zaben gwamna da na 'yan majalisun dokoki a jihohin biyu, yana gudana cikin sauki da kwanciyar hankali kuma ma'aikata hukumar zabe sun isa runfunan zaben kan lokaci har ma suka jira masu kada kuri’a.
Domin Kari