Shugaban kasar Nijer ya aikewa shugaba Muhammadu Buhari sakon taya murna sakamakon lashe zaben da akayi a kasar. Mahamadu Isuhu ya bayyana wannan nasarar a matsayin wata dama da za ta baiwa gwamnatocin kasashen 2 sukunin ci gaba da aiyukan hadin guiwa tsakaninsu.
Kwana daya kenan bayan da shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya karbi takardar shaidar cin zabe a karo na biyu daga hannun shugaban hukumar zaben kasar Farfesa Mahmud Yakubu.
Takaitaccen taron mika takardar shaidar lashe zaben 2019 da shugaban hukumar zaben Najeriya Mahmud Yakubu ya mikawa shugaba Buhari don fara wa’adi na biyu, kuma na karshe a tsarin dokokin Najeriya daga ranar 29 ga watan Mayu.
Bayan da hukumar zaben Najeriya mai zaman kanta INEC ta bayar da sakamakon zaben da ke nuna cewa shugaba Muhammadu Buhari ne ‘yan Najeriya suka sake zaba da kuri’un da suka haura miliyan 15.
Yayin da magoya bayan Jam’iyyar APC ke ci gaba da murnar cin zabe, gamayyar Kungiyoyin kishin al’uma da ci gaban demokaradiyya a Kano sun fitar da sakamakon farko game da yadda zaben shugaban kasa da na ‘yan Majalisar Dokokin Najeriya ya wakana a fadin jihar Kano.
Taron masu ruwa da tsaki kan kin amincewa da sakamakon zaben Filato ta Arewa ya tashi ba tare da cimma matsaya ba.
Jami'iyar APC a jihar Adamawa taki amincewa da sakamakon zaben shugaban kasa a jihar da ya bayyana dan takarar PDP Atiku Abubakar a matsayin wanda ya lashe kuru'u masu yawa a jihar, lamarin da ya haddasa rikici tsakanin shugabannin APC a jihar ta Adamawa.
Yayin da ake cigaba da tattara sakamakon zaben Shugaban kasar Najeriya, zuwa yanzu Shugaba mai ci, Muhammadu Buhari, ya sha gaban Alhaji Atiku Abubakar, babban mai kalubalantarsa na babbar jam'iyyar adawa ta PDP.
Domin Kari