Hukumar zaben Najeriya ta tsaida ranar Asabar 23 ga watan Maris a matsayin ranar da za a kammala zabe a jihohi 6 da ba a kammala zabensu ba.
Jihohin sun hada da Adamawa, Bauchi, Filato, Kano, Sokoto, da kuma Binuwai.
Matakin rashin kammala zaben ya biyo bayan yawan kuri’un da aka soke sun fi tazarar da wanda ya ke kan gaba ya samu idan aka kwatanta da ratar da ya bawa wanda ya ke biye da shi, a cewar hukumar zaben.
Sai dai gwamnan jihar Bauchi kuma dan takarar gwamna a karkashin jam’iyyar APC, Barista Muhammad Abdullahi Abubakar, ya ce yana da kwarin gwiwar cewa jam’iyyarsa ta APC za ta yi nasara a zaben gwamnan da za a kammala.
Shi ma Injiniya Buba Galadima, na jam’iyyar adawa ta PDP ya ce su za su yi nasara muddin ba magudi aka yi ba, yana mai cewa "sai dai idan za ‘a yi amfani da karfin gwamnati a rubuta sakamakon zaben."
Saurari cikakken rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya daga Abuja:
Facebook Forum