Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Jam’iyyar Republican Sun Mai Da Martini Kan Jawabin Biden


'Yar Majalisar dattijan daga Alabama, Katie Britt, wadda ita ce 'yar jam'iyyar Republican mafi karancin shekaru da aka zaba a Majalisar dattijan Amurka, ta soki Shugaba Joe Biden da gwamnatinsa kan iyakoki, yanayin tattalin arzikin Amurka da batutuwan da suka shafi laifuffuka da tsaro a matsayin martani.

Shugabannin Republican sun yaba wa Britt, mai shekaru 42, a matsayin babbar murya a cikin sabbin 'yan Majalisar dokokin Republican.

"A halin yanzu, "Gaskiya, kasar na cikin wani hali – iyalai na cikin damuwa karfin kasarmu fi ya haka." in ji Britt.

A cikin jawabin nata, Britt ta maida hankali sosai kan shige da fice da kan iyaka, tana mai kiran manufofin kan iyaka na Biden "marasa hankali" da "abin kunya.”

“A yanzu haka, babban kwamandan mu ba shi da wani iko. "Amurka ta cancanci shugabannin da suka san mahimmancin kare iyakoki, daidaiton farashi, samar da tsaro mai ƙarfi, su ne ginshiƙan babbar kasa."

Dangane da tattalin arziki, Britt ta kwatanta Biden a matsayin wanda ba shi ma da masaniyar damuwar Amurkawa game da tsadar rayuwa.

Maganan gaskiya, Joe Biden ba zai iya tuna ko da na minti guda lokacin da ya shawo man mota, ya tuka mota ko ma ya tura keken kayan sayen kayan abinci na shago-shago ba," in ji Britt. "A halin yanzu, sauran mu, muna ganin dalar mu kuma mun san ba inda dallar ke zuwa."

"Shugaba Biden bai san abun da ake ciki ba – ko kadan. A karkashin gwamnatinsa, wahalhalun iyalai ya karu, al’ummominmu ba su da tsaro kuma kasarmu ba ta da tsaro,” in ji ta.

An zabi Britt karon farko ne a shekarar 2022, lokacin da kuma ta zama mace ta farko da aka zaba a Majalisar Dattawa daga Alabama. Da amincewar Trump, ta yi nasarar gadan Sanata Richard Shelby na jam’iyyar Republican, wanda a baya ta yi aiki da shi a matsayin shugaban ma’aikata.

Dandalin Mu Tattauna

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG