'Yan tawayen Syria sun hambarar da shugaba Bashar Assad tare da kwace iko da Damascus a ranar Lahadin da ta gabata, lamarin da ya tilasta masa yin gudun hijira tare da kawo karshen mulkin iyalansa na tsawon shekaru da dama da suka shafe sama da shekaru 13 ana yakin basasa a yankin gabas ta tsakiya.
A cikin wani jawabi da ya yi a fadar White House, Biden ya ce rugujewar mulkin dangin Assad na tsawon shekaru da dama, wata “babbar dama ce ga al'ummar Siriya don tsara makomarsu.”
A karon farko a yakin basasar da aka dade ana gwabzawa a kasar, a yanzu gwamnati tana da iko ne kadai da manyan larduna uku cikin14: wato Damascus, Latakia da Tartus.
Taron zai gudana ne a gefen babban taron Doha, wani taron shekara-shekara da ke tattara hancin manyan jami'ai, malamai da shugabannin 'yan kasuwa daga kasashe fiye da 150, domin tattauna batutuwan da suka shafi juna.
A cikin wani sakon da ya wallafa a shafinsa na dandalin sada zumunta na X, Zelenskyy ya ce makamin na jirgin sama maras matuki mai suna "Peklo" - wanda ke nufin "wuta" a harshen kasar Ukraine - yana cin nisan zangon kilomita 700, da karfin gudun kilomita 700 a cikin sa'a guda.
Kotun daukaka kara a Washington ta amince da hujjojin da gwamnatin tarayya ta gabatar cewa TikTok na da hatsari ga tsaron kasa, saboda yana tattara bayanai masu yawa game da masu amfani da shi, da kuma saboda a ƙarshe gwamnatin China tana da karfin iko kan uwar kamfanin, ByteDance.
Wani babban jami’in gwamnatin Ukraine ya kai ziyara Amurka domin kulla alaka da gwamnatin zababben shugaban kasa Donald Trump, wanda ya sha alwashin kawo karshen yakin Rasha a Ukraine da ya kama aiki, kamar yadda kafar yada labaran Ukraine ta ruwaito Ministan Harkokin Wajen kasar ya fada yau Laraba
Shugaban Amurka Joe Biden ya bukaci majalisar dokokin kasar da ta amince da karin dala biliyan 24 domin tallafa wa Ukraine da kuma kara cike ma’adanar makaman Amurka
Shugaban Amurka Joe Biden yayi afuwa ga dansa Hunter, yana mai kokarin ceto dan daga hukuncin dauri a gidan yari akan laifukan da suka shafi bindiga da kuma haraji, inda kuma ya yi fatali da alkawuran da ya dauka a baya, na cewa ba zai yi amfani da karfin ikon shugaban kasa domin amfanin gidansa ba.
A ranar Asabar zababben shugaban Amurka Donald Trump yayi barazanar aza harajin kashi 100 kan gungun kasashen BRICS 9 muddin suka yi gigin yin kafar angulu ga dalar Amurka.
Da sanyin safiyar Larabar nan ne dai yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ta fara aiki, lamarin da ya kawo dakatar da yakin da shugabannin Amurka da na Faransa suka ce zai iya samar da wata hanyar da za a sake yin sulhu a zirin Gaza.
Domin Kari
No media source currently available