dokar da zata dakatar da rufe ofisoshin gwamnati wace zata bada dama a samarwa gwamnati kudaden da zata kashe na wucin gadi har zuwa watan Maris.
An kada kuri’un amincewa 366 da suka rinjayi na kin amincewa 34, inda dan majalisa guda kuma bai da kowane ra’ayi. Dukkanin kuri'u 34 da suka nuna adawa da kudirin na 'yan jam’iyyar Republican ne.
Jami'an Ukraine sun ce harin ya biyo ne bayan harin makami mai linzami da Rasha ta fara kai wa a Kyiv.
Karar wadda aka shigar a ranar 19 ga watan Maris a Kotun Gunduma ta Amurka da ke Kudancin Florida, ta zargi Stephanopoulos ABC News da yin munanan kalamai kan Trump tare da mummunar manufa da kaucewa gaskiya.
A bara Birtaniya ta bayyana cewa za ta shiga cikin wannan babbar yarjejeniyar ciniki tun bayan ficewar ta daga Tarayyar Turai.
Sanya Karin lokacin agogo da sa’a daya a gaba a cikin hunturu, da kuma ragewa baya da sa'a guda a lokacin bazara, na da manufar kara tsawaita wuni a cikin watannin bazara, to amma kuma an daɗe ana cece-kuce da muhawara kan lamarin.
A daren jiya Laraba, zababben Shugaban Amurka Donald J. Trump ya zabi Kari Lake ta jagoranci Muryar Amurka (VOA)
Yayinda Amurka ta kashe sama da dala miliyan takwas a matsayin gudunmawa a bangaren kiwon lafiya a Najeriya, ta kara jaddada kudirinta na taimakawa wajen gina kasar a matsayin babbar kasa mai kwakkwaran tsarin kiwon lafiya, yaki da cin hanci da tabbatar da gaskiya da adalci
Kada kararrawar wata alama ce dake nuni da budewa ko rufe hada-hadar yini a babbar kasuwar hannayen jari ta duniya, kuma ana yiwa hakan kallon karramawa.
'Yan tawayen Syria sun hambarar da shugaba Bashar Assad tare da kwace iko da Damascus a ranar Lahadin da ta gabata, lamarin da ya tilasta masa yin gudun hijira tare da kawo karshen mulkin iyalansa na tsawon shekaru da dama da suka shafe sama da shekaru 13 ana yakin basasa a yankin gabas ta tsakiya.
A cikin wani jawabi da ya yi a fadar White House, Biden ya ce rugujewar mulkin dangin Assad na tsawon shekaru da dama, wata “babbar dama ce ga al'ummar Siriya don tsara makomarsu.”
Domin Kari
No media source currently available