Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Turkiyya, Rasha, Iran Za Su Gana A Qatar Kan Rikicin Syria


APTOPIX Iran Turkey Russia Syria
APTOPIX Iran Turkey Russia Syria

Taron zai gudana ne a gefen babban taron Doha, wani taron shekara-shekara da ke tattara hancin manyan jami'ai, malamai da shugabannin 'yan kasuwa daga kasashe fiye da 150, domin tattauna batutuwan da suka shafi juna.

Kasashen Turkiyya da Rasha da Iran za su gana a Qatar a karshen wannan makon, domin tattauna martanin da za su mayar dangane da wani gagarumin ci gaba da ‘yan tawaye suka yi, wanda ya kawo sauyi sosai a fagen dagar rikicin kasar Syria na tsawon shekaru 13.

Taron zai gudana ne a gefen babban taron Doha, wani taron shekara-shekara da ke tattara hancin manyan jami'ai, malamai da shugabannin 'yan kasuwa daga kasashe fiye da 150, domin tattauna batutuwan da suka shafi juna.

Ministan harkokin wajen Turkiyya Hakan Fidan "zai gana da ministocin Rasha da na Iran ... domin wani taro karkashin tsarin Astana", kamar yadda wata majiya a ma'aikatar harkokin wajen kasar ta shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP.

Rasha da Iran da ke goyon bayan shugaban Syria Bashar Assad, sun kaddamar da tsarin Astana tare da Turkiyya - da ke goyon bayan wasu kungiyoyin 'yan tawaye - a Astana babban birnin Kazakhstan a shekara ta 2017. Manufarsu ita ce samar da mafita ta siyasa ga yakin basasar.

Rasha da Turkiyya sun sami nasarar kulla yarjejeniyar tsagaita bude wuta a shekara ta 2020, wadda ta dakile akasarin wutar rikicin yakin, wanda ya baiwa Assad damar iko kan dukkan manyan biranen kasar da kuma kusan kashi 70% na yankin kasar Siriya.

Sai dai a wani gagarumin farmaki da suka kai a cikin makon da ya gabata, 'yan tawayen Islama na Hayat Tahrir al-Sham, sun kwace birnin Aleppo, birni na biyu mafi girma a kasar Syria, inda suka ci gaba suka kuma kwace Hama, tare da matsawa kusa da birnin Homs na uku mafi girma a Syria.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG