A yau Lahadi shugaban addini a Iran Ayatollah Ali Khamenei ya yi kira ga Amurka da ta dage duk wasu takunkumai a ka Iran indai har Washington na son Tehran ta ruguza shirinta na kera makaman nukiliya.
Shugaban Amurka Joe Biden, ya yi alkawarin cewa Amurka za ta yi matukar dada taka rawa a harkokin duniya a tsawon wa'adinsa, ya na mai kawo karshen abin da ya kira "shekaru hudu na yin watsi da kuma amfani da harkokin waje ba bisa ka'ida ba" da tsohon Shugaba Donald Trump ya yi.
Majalisar dattawan Amurka zata fara shari’a mai cike da tarihi ta tsige tsohon shugaban Amurka Donald Trump a wannan wata, inda zata kammala da kada kuri’a da zata yanke hukumci a kan ko yana da alhakin ingiza tarzoma a kan majalisar dokoki a ranar 6 ga Janairu.
Shugaban Amurka Joe Biden na shirin karbar bakuncin wasu sanatoci 10 ‘yan jam’iyyar Republican don tattaunawa yau Litinin game da wani sabon zagaye tallafin tattalin arzikin coronavirus.
Lauyoyin tsohon shugaban sun kasa cimma matsaya akan dabarar da ta fi dacewa don kare shi a majalisar dattawan kasar.
Cibiyar yaki da cututtuka masu yado ta Amurka ta CDC ta fitar da wani umarnin gama-gari da yammacin ranar Juma’a na tilasta saka kyallen rufe huska a cikin kowane nau’in sufurin jama’a da zai fara aiki cikin daren gobe Litinin, yayin da kasar ke kara samun dubban mace mace.
Gwamnatin sabon shugaban Amurka Joe Biden zata dakatar da tsarin banbance tsakani sha’anin cikin gida da na kasashen waje da aka saba da shi a Amurka, wurin tinkarar batutuwan barazana ga tsaron kasa.
A karon farko tun bayan da aka rantsar da shi, shugaban Amurka Joe Biden ya yi magana da shugaban Rasha Vladimir Putin, inda ya bayyana damuwar Amurka kan wasu batutuwa.
Shugaba Joe Biden ya gana da 'Yan majalisar dattawan Amurka a wanI yunkuri na cimma matsaya dangane da tallafin rage radadin COVID-19 a kasar.
Wasu ‘kusoshin jam’iyyar Republican a majalisar dattawan Amurka, sanata Marco Rubio da sanata Mitt Romney, a jiya Lahadi sun nuna rashin amincewar su da shirin sabuwar shari’ar sake tsige tsoho shugaban Amurka Donald Trump.
Firai ministan Birtaniya Boris Johnson ya fadawa shugaba Joe Biden cewa, a shirye yake ya bude sabon babi a yarjejeniyar kasuwancin Amurka da Birtaniya.
Rahotannin sun nuna cewa cutar coronavirus ce ta yi sanadiyar mutuwar Larry King, wanda shirinsa na "Larry King Live" na gidan talabijin din CNN ya tattaro miliyoyin 'yan kallo daga fadin duniya.
Domin Kari
No media source currently available
A jawabin da ya gabatar, shugaban kasar, Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa na samun nasarar yaki da ta’addanci da kuma ‘yan fashin daji. Jawabin shugaban ya zo ne adaidai lokacin da matasa a wasu sassan Najeriya suka gudanar da zanga-zangar matsin rayuwa.
Mataimakan ‘yan takarar shugaban kasa, Tim Walz na jam’iyyar Democrat da kuma JD Vance na Republican sun fafata a muhawarar su ta farko wacce kuma ita ce kadai da za su yi kafin zaben shugaban kasa a watan Nuwamba. Ga fasaarar rahoton Tina Trinh daga New York.
A bana, sau biyu ana yin yunkurin halaka dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Republican Donal Trump. Muryar Amurka ta ji ta bakin wasu Amurka da suka mallaki bindiga wadanda suka ce yunkurin halaka Trump din bai sauya matsayarsu ba a game day dokokin mallakar bindiga a Amurka.