Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Zata Karfafa Matakan Saka Takunkumi A Cikin Motoci Da Jirage


Matafiya saye da takunkumai
Matafiya saye da takunkumai

Cibiyar yaki da cututtuka masu yado ta Amurka ta CDC ta fitar da wani umarnin gama-gari da yammacin ranar Juma’a na tilasta saka kyallen rufe huska a cikin kowane nau’in sufurin jama’a da zai fara aiki cikin daren gobe Litinin, yayin da kasar ke kara samun dubban mace mace.

Umarnin da zai fara aiki da karfe 11 da minti 59 na daren Litinin saura dakika a shiga ranar Talata, zai bukaci matafiya su saka takunkumin rufe huska a cikin jirgin sama da jirgin ruwa da na kasa da motocin bos da taxi da kowane iri motocin jama’a, za a kuma bukaci a saka takunkumin a wuraren daukar ababen hawa kamar tashoshin mota da filayen jiragen sama da tashoshin jiragen kasa da na ruwa.

A ranar 21 ga watan Janairu, shugaba Joe Biden ya umarci hukumomin gwamnati su gaggauta daukar matakan saka takunkumi a filayen saukar jiragen sama da kuma cikin jiragen kasuwa da cikin jirgin kasa da jiragen ruwa na jama’a da kananan jiragen ruwa da bos bos da duk sufurin jama’a.

A karkashin shugaba Donald Trump wanda ya kammala mulki a ranar 20 ga watan Janairu, hukumar yaki da cuta mai yadon ta nemi bada umarnin tilasta saka takunkumi a cikin sufuri amma hakan bai yiwuwa ba, a maimakon haka sai hukumar ta bada shawarwari masu karfi a kan saka takunkumin.

Kungiyar kamfanonin jiragen sama ta Amurka ta fadawa Biden a cikin wannan wata cewa nan gaba zata hana dubban fasinjoji bulaguro da suka ki biyewa umarnin saka takunkumin.

XS
SM
MD
LG