Ana cigaba da samun bayanan yadda rayuwa take a duniyar sama.
Amurka na gab da samun mace-mace rabin miliyan sakamakon cutar COVID-19, da karin mace-mace da ke da alaka da coronavirus fiye da kowacce kasa, a cewar cibiyar samar da bayanan coronavirus ta Jami’ar Johns Hopkins.
Amurka ta sake komawa cikin yarjejeniyar Paris a hukumance bayan da gwamnatin Trump ta fice daga yarjejeniyar ta sauyin yanayi, tana mai cewa shirin ya yi matukar tsada ba zata yi aiki da shi ba.
Shugaban Amurka Joe Biden ya yi alkawarin ba da tallafin dala biliyan hudu domin a kara kaimi wajen samar da allurar rigakafin cutar COVID-19 ga kasashe marasa galihu.
Wani hadarin tarihi na lokacin sanyi da ya kara tsananin sanyi a akalla rabin fadin Amurka, ya sa sama da mutum miliyan biyu da rabi a Texas sun rasa wutar lantarki.
Majalisar Dattawan Amurka, ta wanke Donald Trump a yunkurin tsige shi da aka yi a karo na biyu cikin shekara guda, inda ‘yan Republican suka hana a dora masa laifi mummunan harin da magoya bayansa suka kai a ginin majalisar dokokin kasar.
Majalisar dattawan Amurka ta kada kuri’ar bada sammacin gayyato shaidu su bada bahasi a wannan shari’ar tsige tsohon shugaban kasa Donald Trump.
Majalisar dattawan Amurka ta ci gaba da zama da safiyar yau Asabar a matsayin kotu a kan batun tsige tsohon shugaban kasa Donald Trump.
Masu gabatar da kara a shari’ar tsige tsohon shugaban Amurka Donald Trump a Majalisar Dattawan kasar sun koma yau Alhamis don gabatar da hujjojin cewa Trump ne ya tunzura mummunan farmakin da aka kai kan ginin Majalisar a watan jiya.
Wata shararriyar mawakiyar Amurka Mary Wilson da tayi fice a cikin fitattun mata mawaka uku da ake kira da The Supremes a cikin shekarun 1960 ta mutu tana da shekaru 76.
Gabanin babban taron Tarayyar Afirka, shugaban Amurka Joe Biden ya ce gwamnatin kasar ta dukufa wajen aiki tare da Tarayyar Afirka domin cimma manufofinsu na samun kyakkyawar rayuwa da makoma.
Yau za'a fara sauraron karar sake tsige tsohon shugaban Amurka Donald Trump a majalisar dattawan Amurka.
Domin Kari
No media source currently available
A jawabin da ya gabatar, shugaban kasar, Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa na samun nasarar yaki da ta’addanci da kuma ‘yan fashin daji. Jawabin shugaban ya zo ne adaidai lokacin da matasa a wasu sassan Najeriya suka gudanar da zanga-zangar matsin rayuwa.
Mataimakan ‘yan takarar shugaban kasa, Tim Walz na jam’iyyar Democrat da kuma JD Vance na Republican sun fafata a muhawarar su ta farko wacce kuma ita ce kadai da za su yi kafin zaben shugaban kasa a watan Nuwamba. Ga fasaarar rahoton Tina Trinh daga New York.
A bana, sau biyu ana yin yunkurin halaka dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Republican Donal Trump. Muryar Amurka ta ji ta bakin wasu Amurka da suka mallaki bindiga wadanda suka ce yunkurin halaka Trump din bai sauya matsayarsu ba a game day dokokin mallakar bindiga a Amurka.