Tsohon shugaban yana fuskantar zargin ingiza tarzoma mai alaka da tura dinbim magoya bayansa zuwa ginin majalisun kasar, yayin da ‘yan majalisa suke zaman tabbatar da sakamakon kuru’un da suka baiwa shugaba Joe Biden nasarar shiga ofis.
Masu kula da aiwatar da shari’ar tsigewar sune ‘yan majalisar wakilai da zasu gabatar da batun tsige tsohon shugaban kasa Trump a gaban majalisar dattawa.
Wadannan wakilai tara sune zasu gabatar da jawabai, tamkar masu shugar da kara a dakin kotu, da zummar neman kashi biyu cikin uku na ‘yan majalisar dattawa ko mutum 67 su kada kuri’ar amincewa da tsige shi.
Trump na fuskantar zargin aikata laifi guda ne na ingiza tarzoma a ranar 6 ga watan Janairu a kan majalisun kasar yayin da suke zaman bai daya na tabbatar da sakamakon zaben shugaban kasa na shekarar 2020.