A cigaba da shirye shiryen bankwana da ake ma marigayiya Ruth Bader Ginsburg ta Kotun Kolin Amurka, an fara ma ta gaisuwar girmamawa ta karshe.
Jiya Talata adadin wadanda cutar coronavirus ta kashe a Amurka ya kai 200,000 adadin da ya zarce na kowacce kasa a duniya, da kwararrun harkokin lafiya ke cewa adadin zai ci gaba da karuwa zuwa dubbai cikin ‘yan watanni masu zuwa.
A jiya Talata ne shugabanin kasashen duniya suka fara gabatar da jawaban su a taron kolin Majalisar Dinkin Duniya na cikon shekaru 75. da ake gabatarwa ta yanar gizo sakamakon cutar coronavirus da take ci gaba da yin barazana ga duniya.
Cibiyar Yaki Da Cututtuka Masu Yado Ta Amurka ta janye wani karin bayanin da ta yi ranar Jumma'a kan yadda cutar corona ke yaduwa. Ta ce ana bukatar kara tantance bayanin.
A jiya Litinin shugaban Amurka Donald Trump ya ce ya rage yawan sunayen mutanen da yake so ya zaba alkalin kotun koli zuwa mutum biyar, kana ana sa ran zai sanar da wanda zai maye gurbin marigayiya Mai shari’a Ruth Bader Ginsburg a ranar Juma’a ko Asabar.
A yau litinin Amurka za ta saka takunkumi akan mutane fiye da 24 da wadanda ke da hannu a shirin nukiliya da makamai masu linzami na Iran.
Shugaban Amurka Donald Trump, ya ce zai gabatar da mace wadda za ta zama Alkali a babbar Kotun Kolin Amurka, biyo bayan mutuwar mai shari’a Ruth Bader Ginsburg.
Amurka mayar da dukkan takunkumin Majalisar Dinkin Duniya MDD kan kasar Iran, ciki har da takunkumin makamai kamar yadda wata sanarwa da sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ya fitar ranar Asabar.
Ana ci gaba da nuna alhini dangane da rasuwar Mai Shari’a a kotun kolin Amurka Justice Ruth Bader Ginsburg, wacce ta rasu a ranar Juma’a tana mai shekara 87.
Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ya isa kasar Brazil ranar Juma’a, inda ya ziyarci cibiyar tantance ‘yan gudun hijirar kasar Venezuela, yayin da ya yi kira ga dimokaradiya da kuma shugaban kasa Nicolas Maduro ya sauka daga kan Mulki.
Alkali Ruth Ginsburg wadda ta dade a matsayin alkalin kotun Amurka ta rasu yau jumma'a bayan ta yi fama da rashin lafiya na tsawon lokaci.
Domin Kari
No media source currently available
A jawabin da ya gabatar, shugaban kasar, Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa na samun nasarar yaki da ta’addanci da kuma ‘yan fashin daji. Jawabin shugaban ya zo ne adaidai lokacin da matasa a wasu sassan Najeriya suka gudanar da zanga-zangar matsin rayuwa.
Mataimakan ‘yan takarar shugaban kasa, Tim Walz na jam’iyyar Democrat da kuma JD Vance na Republican sun fafata a muhawarar su ta farko wacce kuma ita ce kadai da za su yi kafin zaben shugaban kasa a watan Nuwamba. Ga fasaarar rahoton Tina Trinh daga New York.
A bana, sau biyu ana yin yunkurin halaka dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Republican Donal Trump. Muryar Amurka ta ji ta bakin wasu Amurka da suka mallaki bindiga wadanda suka ce yunkurin halaka Trump din bai sauya matsayarsu ba a game day dokokin mallakar bindiga a Amurka.