Jiya Laraba ne, a wajen babban taronsu a birnin Philadelphia, shugabannin jam’iyyar Democrat suka gabatar da jawaban da ke tabattarda cewa Hillary Clinton ce zasu tsaida a matsayin 'yar takarar shugabar kasar Amurka ba Donald Trump baa zaben da za'a gudanar a wannan shekara .
Shugaban Amurka Barack Obama da Mataimakinsa Joe Biden, sun yi jawabi a rana ta uku a babban taron Democrat da ake yi a Philadelphia, inda Biden ya jinjina ma na gaba da shi, Shugaba Barack Obama, ya kuma jaddada cancantar 'yar takarar jam'iyyarsu a zaben shugaban kasar na 2016, Hillary Clinton.
A jawabinsa na farko a matsayinsa na dan takarar zama Shugaban Amurka karkashin jam'iyyar Republican a hukumance, Donald Trump ya yi amfani da lafazin da ke nuna akwai matukar bukatar daukar matakin gaggawa, kan tashe-tashen hankulan da ke faruwa a Amurka kwanan nan, sannan ya jaddada cewa a karkashin Shugabancinsa, Amurka za ta zama kasa mai bin doka da oda.
Yayin da aka kaddamar da yakin zaben shugaban kasa zagaye na biyu jiya Talata a Jamhuriyar Nijar, kawancen jam’iyyun adawar kasar da ake kira COPA ya bayyana janyewa daga wannan fafatawa da za a yi ranar 20 ga watan Maris.
Tunda aka yi zaben kasar Nijar ranar 21 ga watan Fabrairu sai jiya kotun tsarin mulkin kasar ya tabbatar da sakamakon zaben tare da yin kwaskwarima
Yayinda zaben shugaban kasar Nijar zagaye na biyu ke karatowa shugabannin gamayyar jam'iyyun siyasa da suke goyon bayan Hamma Ahmadou a zaben mai zuwa sun kai masa ziyara a kurkuku
Daya daga cikin jam'iyyun hamayya da suka ce sun tsayar da Hamma Ahmadu a matsayin dan takararsu a zaben shugabankasar Jamhuriyar Nijar ta ce ba da yawunta aka cimma matsaya ba akan Hamma ba.
Ba za'a iya jin sakamakon zaben Shugaban kasar Nijar da na 'yan Majalisu ba sai nan da wata daya bayan an sake kara zaben 'yada kanin wani tsakanin Mahamadu Issoufou da Hama Amadou, inji hukumar zaben kasar.
Bisa alamu babu wani dan takara a zaben Nijar da ya ci kujerar shugaban kasa kai tsaye a zagayen farko.
Domin Kari