Labarin da muka samu daga kasar Nijar na nuni da cewa sai an yi zagaye na biyu a zaben kasar kafin a tabbatar da shugaban kasa.
A zagayen farko da aka yi ranar Lahadi da ta gabata shugaban kasar mai ci yanzu wanda ya yi ikirarin zarcewa a zagayen farko bai kai labari gida ba domin bai samu kashi hamsin na kuri'un da aka kada ba kamar yadda kundun tsarin mulkin kasar ya tanada.
Yanzu dai sai asa ido a gani wace rana hukumar zaben kasar zata tsayar domin gudanar da zaben zagaye na biyu wanda shi ne zai fitar da shugaban kasa.
Hamma Ahmadu na jam'iyyar MODEN Lumana wanda har yanzu yana kurkuku shi ne kuma ya zo na biyu a wannan zgayen farkon mai 'yan takara goma sha biyar