"Wannan babban taro namu na faruwa a daidai lokacin da kasar ke cikin mawuyacin hali. Hare-haren da ake kaiwa kan 'yansandanmu da hare-haren ta'addancin da ake kaiwa kan biranenmu, na barazana ga tsarin rayuwarmu. Duk wani dan siyasar da ya kasa gane hakan, bai kamata ya jagoranci kasarmu ba," a cewarsa.
Trump ya zayyana alkaluman da ke nuna karuwar aikata manyan laifuka manyan birane da dama, ciki har da Washington DC, da Baltimore, wadanda Trump ya ce sun ga karuwar kisan kai na 50% da 60% cikin shekara guda da ta babata.
"A jahar Chicago da Shugaban kasa ya fito, mutane sama da 2,000 ne harbe-harbe su ka rutsa da su a wannan shekarar kawai. Kuma an hallaka mutane sama 3,600 a birnin na Chicago tun bayan da ya hau gadon mulki," a cewar Trump.
Gama da auna 'yan sanda da aka yi ta yi a Baton Rouge na jahar Louisiana da Dalas na jahar Texas, Trump ya bayyana hakan da hari kan dukkan AMurkawa," sannan ya zargi Shugaba Obama da amfani da matsayinsa na Shugaban kasa wajen raba mutane bisa ga jinsi da kuma launi.
"Duk wani matakin da zan dauka, sai na tambayi kaina: Shin zai kyautata rayuwar matasa a Baltimore, da Chicago, da Detroit, da Ferguson; wadanda su ma ke da damar cimma rayuwar da su ke hankoro, kamar sauran yara a Amurka" a cewar Trump.