Yayin da aka kaddamar da yakin zaben shugaban kasa zagaye na biyu jiya Talata a Jamhuriyar Nijar, kawancen jam’iyyun adawar kasar da ake kira COPA ya bayyana janyewa daga wannan fafatawa da za a yi ranar 20 ga watan Maris.
Tunda aka yi zaben kasar Nijar ranar 21 ga watan Fabrairu sai jiya kotun tsarin mulkin kasar ya tabbatar da sakamakon zaben tare da yin kwaskwarima
Yayinda zaben shugaban kasar Nijar zagaye na biyu ke karatowa shugabannin gamayyar jam'iyyun siyasa da suke goyon bayan Hamma Ahmadou a zaben mai zuwa sun kai masa ziyara a kurkuku
Daya daga cikin jam'iyyun hamayya da suka ce sun tsayar da Hamma Ahmadu a matsayin dan takararsu a zaben shugabankasar Jamhuriyar Nijar ta ce ba da yawunta aka cimma matsaya ba akan Hamma ba.
Ba za'a iya jin sakamakon zaben Shugaban kasar Nijar da na 'yan Majalisu ba sai nan da wata daya bayan an sake kara zaben 'yada kanin wani tsakanin Mahamadu Issoufou da Hama Amadou, inji hukumar zaben kasar.
Bisa alamu babu wani dan takara a zaben Nijar da ya ci kujerar shugaban kasa kai tsaye a zagayen farko.
Yayinda jama'ar kasar Jamhuriyar Nijar ke jiran sakamakon zabukan da suka yi shugabannin addinai na cigaba da kiran 'yan kasar su rungumi zaman lafiya ta karbar duk wanda aka bayyana a matsayin shugaban kasa
A yayin wani taro manema labarai da tayi a cibiyar kungiyar NPCR ta Nuhu Muhammadu Arzika kungiyar sa ido da ake kira ONET ta yaba da yanayin kwanciyar hankalin da aka gudanar da zaben Jamhuriyar Nijar
Sakamakon zaben shugaban kasar Jamhuriyar Nijar, na baya bayannan na nuni da cewa, shugaban kasa mai ci Mahamadou Issofou har yanzu yana kan gaba.
Domin Kari