A jawabinsa, Shugaba Obama ya yi magana akan irin kalubalan da ya fuskanta a lokacin da yayi yakin neman zaben shugaban kasa inda kuma ya nuna nasarorin da ya cimma a lokacin mulkinsa ya kuma bayyana cewa Hillary Clinton ita ce ‘yar takara a wannan shekarar da ta yi imanin cewa idan mutane dabam-dabam suka hada kai za a samu cigaba a Amurka.
Ya kuma ce babu mutumin ko macen da ta taba cancanta ta shugabanci Amurka kamar Clinton, wadda ta yi aiki a matsayin sakatariyar harkokin wajen Amurka a wa’adin aikinsa na farko.Haka kuma shugaba Obama ya caccacaki dan takaran shugaban kasa na jam'iyyar republicans, Donalda Obama:
Shugaba Obama yake cewa: "Donald Trump baya da komai da zai tsinanawa Amurka, illa surutun iska kawai. Yana jin idan ya tsorata mutane sosai, zasu iya zabensa, kuma wannan ma wata caca ce da Trump ba zai ci ba, tunda yana neman rena wayon Amurkawa." Ko bayan shi Shugaba Obama, sauran wadanda suka yi jawabbai jiya sun hada da mataimakinsa Joe Biden da kuma mutumen da ita Hilary ta dauko do ya zamar mata mataimaki, Tim Kaine. A yau ne ake sa ran cewa ita kanta Hilary Clinton zata fito tayi jawabin amincewa da karbar zama 'yar takara ta jam'iyyar Democrats din.