Shugaban Najeriya Mohammadu Buhari ya shiga jerin kasashen duniya da ke yiwa sabon zababben shugaban kasar Amurka Donald Trump Murna.
Donald Trump shine ya zama zababben shugaban kasar Amurka.
Zaben da aka yi jiya a nan Amurka ya bada sakamakon bazata saboda masu bin digdigin alamuran siyasa sun yi kiyasin cewa Hillary Clinton ce zata yi galaba
Ko bayan shugaban kasa, har ila yau a jiyan Amurkawa sun jefa kuri’un zaben ‘yan Majalinsun su na Tarayya, kuma duk sakamakon da aka samu na iya sauya shugabancin majalisun a tsakanin jam’iyyun biyu manya na Democrats da Republican.
Har yanzu ana ci gaba da karban sakamakon zaben shugaban kasa na Amurka da aka yi jiya na wannan shekara ta 2016, kuma izuwa yanzu ‘yan takaran, Hilary Clinton ta Democrats da Donald Trump duk suna ci gaba da lashe jihohin da aka yi zaton zasu lashe.
A tarihin Amurka mutanen Democrats sun fi tausayin talaka da mai tasowa fiye da 'yan Repubiican haka kuma sun fi muamala da kasashen Afirka.
A jamhuriyar Nijar masu nazarin harkokin siyasa sun kira 'yan siyasar Afirka da su koyi yadda ake gudanar da zabe a Amurka cikin natsuwa da lumana
Tun kafin ranar zaben na Amurka 'yan Najeriya da dama suke goyon bayan Hillary Clinton ta jam'iyyar Democrat wadda suke ganin tafi Donald Trump saukin kai da son zaman lafiya
A yayin da Amurkawa ke fitowa kwansu da kwarkwatarsu domin kada kuri’un zaben sabo ko sabuwar shugaban kasa, mai cike da dinbin tarihi.
Domin Kari