Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bayan Zaben Shugaban Kasa Amurkawa Sun Zabi 'Yan Majalisu


Ginin Majalisar Amurka da ake kira Capitol
Ginin Majalisar Amurka da ake kira Capitol

Ko bayan shugaban kasa, har ila yau a jiyan Amurkawa sun jefa kuri’un zaben ‘yan Majalinsun su na Tarayya, kuma duk sakamakon da aka samu na iya sauya shugabancin majalisun a tsakanin jam’iyyun biyu manya na Democrats da Republican.

Kafin a fita zaben a jiya, dua majalisun biyu – ta Dattawa da ta wakilai – suna karkashin rikon jam’iyyar Republicans ne, abinda yassa suka rinka adawa da shirye-shiryen dokokin da shugaban Amurka na yanzu Barack Obama ya sha aika musu, har aka zo a aka sami cikas a tsakanin fadar shugaban kasar da su ‘yan majalisan.

Kujerun da ake takara akansu a wannan zaben sun hada da kujeru 34 na Majalisar Dattawa wadda ke da jimillar kujeru 100 da kuma daukacin dukkan kujeru 4r35 na Majalisar wakilai. ‘Yan jam’iyyar Democrats na fatar samun isassun kujerun da zasu basu rinjaye don su chanja halin da ake ciki a yanzu inda suke da kujeru 46, abokan adawarsu na Republican kuma suna da 54.

XS
SM
MD
LG